Jamus: Tallafi wa jam'aa saboda yakin Ukraine
August 10, 2022Talla
Dan siyasar na jam'iyyar FDP wanda ya bayyana haka a wani taron manmema labarai ya ce suna shirin yin wani kudiri na dokar biyan diyya wanda zai tanadi kara yawan tallafin yara da kuma rage haraji. Halin rayuwa a Kasar ta Jamus ya kara yin tsanani tun bayan da aka soma yaki tsakanin Ukraine da Rasha, abin da ya haddasa tsadar rayuwa mafi muni da ba a taba gani ba a cikin shekaru da dama.