1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala taron jam'iyyar Democrat ta Amirka

Suleiman BabayoJuly 29, 2016

Hillary Clinton ta yi jawabi a babban taron jam'iyyar Democrat a matsayin 'yar takara a zaben shugaban kasa na Amirka da zai gudana a wannan shekara.

https://p.dw.com/p/1JXbN
Hillary Clinton Democratic National Convention USA Rede
Hoto: Reuters/G. Cameron

A Amirka Hillary Clinton ta yi jawabi a rana ta karshe bisa taron jam'iyyar Democrat inda ta karbi ragama na takara wa jam'iyyar a zaben shugaban kasa na watan Nuwamba da ke tafe. Ita dai Clinton ta kafa tarihi wajen zama mace ta farko da wata babbar jam'iyya a kasar ta tsayar domin takara a zaben shugaban kasa.Hillary Clinton ta kasance tsohuwar sanata kana tsohuwar sakatariyar harkokin waje kuma mata ga tsohon shugaban kasa Bill Clinton.

Yanzu Hillary Clinton ta jam'iyyar Democrat 'yar shekaru 68 da haihuwa za ta fafata da da Donald Trump na jam'iyyar Republican a zaben ranar 8 ga watan Nuwamba mai zuwa, kuma duk wanda ya samu nasara zai daukin madafun ikon kasar ta Amirka daga hannun Shugaba Barack Obama a watan Janairu na shekara mai zuwa ta 2017.