Yakin neman zaben Kenya ya shiga matakin karshe
August 6, 2017A kasar Kenya an shiga matakin karshe na yakin neman zaben da zai gudana a ranar Talata mai zuwa, inda 'yan takara ke karakaina bisa neman kuri'u daga mutanen kasar. Manyan 'yan takara a zaben shugaban kasa biyu ke kan gaba Shugaba Uhuru Kenyatta da kuma jagoran 'yan adawa Raila Odinga.
Sai dai akwai zaman zullumi na yiwuwar samun tashin hankali, musamman sakamakaon yadda 'yan takarar suke kut-da-kut. Yayin da zaben ke karatowa gwamnatin ta Kenya ta fatattaki wasu 'yan kasashen ketare biyu wadanda suke aiki a yakin neman zaben jagoran 'yan adawa Raila Odinga. Turawan sun kasance 'yan kasashen Amirka da Canada.
Babban abin da mutane suke jin tsoro a kasar ta Kenya na zama maimaita tashin hankali da aka samu a zaben shekara ta 2007, lamarin da ya kai ga mutuwar fiye da mutane 1000.