Yan adawa a Kenya sun bukaci a gudanar da zabe kafin lokacin sa
November 24, 2005Yan adawa na kasar Kenya sun bukaci shugaba Mwai Kibaki daya shirya gudanar da zabe na gama gari kafin lokacin da aka tsara a can baya wato shekara ta 2007.
Wannan dai kira daga bangaren yan adawar yazo ne kwana daya bayan shugaba Kibaki ya sauke dukkannin jami´an majalisar zartarwar gwamnatin tasa, a sakamakon kaye daya sha a lokacin zaben raba gardama akan sabon kundin tsarin mulki na kasar.
A cikin wata takarda da jam´iyyun suka aikewa yan jaridu sun shaidar da cewa sakamakon zaben raba gardamar na nuni a fili cewa da yawa daga cikin alummar kasar sun dawo daga rakiyar gwamnatin ta Kibaki.
Idan dai za a iya tunawa da yawa daga cikin alummar kasar ta Kenya sun kada kuriun su na kin amincewa da wannan sabon kundin tsarin mulkin a ranar litinin din nan data gabata, wanda hakan ke a matsayin wani babban koma baya ga shugaba Mwai Kibaki a siyasan ce.
Rahotanni dai sun nunar da cewa wannan zabe na raba gardama akan sabon daftarin tsarin mulkin da alama ka iya kawo rarrabuwar kawuna a tsakanin kabilun kasar.