'Yan adawa za su kalubalanci Yahya Jammeh
October 31, 2016Talla
Adama Barrow dan shekaru 51 jagoran jam'iyyar UDP shi ne hadin gwiwar jam'iyyun siyasar na adawa guda bakwai suka wakilta ya tsaya takara a zaben na watan Disamba da ke tafe,wanda shi ne karo na biyar ke'nan da Yahya Jammey zai yi takara.Jammeh wanda ya zo kan karagar mulki bayan wani juyin mulkin a shekara ta 1994 kafin ya rikide ya koma farar hula kungiyoyi masu fafutuka da na 'yan adawar kasar da kuma 'yan jaridu na zarginsa da take hakin bil Adama.