1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawan Gambiya na rasuwa a hannun huma

Yusuf BalaAugust 23, 2016

Rasuwar dan adawa ta bayan nan ta kasance ta biyu cikin watanni biyar, lamarin da ke faruwa watanni kafin zaben da ake sa ran Shugaba Yahya Jammeh zai yi tazarce.

https://p.dw.com/p/1JnqJ
Yahya Jammeh 2006
Hoto: picture-alliance/AP/Rebecca Blackwell

Wani mamba a jam'iyyar adawa a kasar ta Gambiya ya rasu a hannun mahukunta, kamar yadda jam'iyyar UDP mai adawa ta bayyana. Abin da ya sanya Majalisar Dinkin Duniya da Amirka da Faransa suka nemi a gudanar da bincike kan lamarin.

Rasuwar dan adawar dai ta kasance ta biyu cikin watanni biyar, lamarin da ke faruwa watanni kafin zaben watan Disamba da ake sa ran Shugaba Yahya Jammeh zai yi tazarce a karo na biyar.

Jami'in jam'iyyar a wani yanki na kasar Ebrima Solo Kurumah, ya rasu kamar yadda mataimakin shugaban jam'iyyar ta UDP Dembo Bojang ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP. Jam'iyyar dai ta bayyana cewa za ta tabbatar da ganin cewa likitoci sun gudanar da bincike kan musabbabin rasuwar mambansu kafin a kai ga mikawa iyalan mamacin wadanda tun da mahukunta suka tsrae shi ba su bari ba sun gana. Shugaba Jameh dai ya dare kan karagar mulki tun a shekarar 1994 bayan juyin mulki.