'yan Adawan Kenya sunyi watsi da bukatar kafa gwamnatin Haɗin kan ƙasa
January 5, 2008Shugaba Mwai Kibaki yayi kira dangane da kafa gwamnatin hadin kann ƙasa a Kenya,domin kawo karshen rigingimun daya kashe ɗaruruwan mutane a wannan kasa.Shugana Kenmyan yayi wannan kiran ne bayan ganawarsa da mataimakin sakatariyar harkokin wajen Amurka kann harkokin Afrika Jedanyi Frazer a birnin Nairobi.To sai dai bayan ganawar jakadan Amurkan da shugaban Adawa Raila Odinga,ya bayyana masa cewar babu sauyin matsayi adangane da bukatar da suka gabatar..“Odinga yace Gwamnatin Amurka tana sane da yadda lamura suka gudana,dominakwai masu sa ido Amurkawa alokacin.Kuma suna sane da yadda aka tabka magudi acikin zaben.Faransa ta kirashi fashi da makami wa Democradiyya.Abunda muke kokarin yi shine warware matsalar.Su kuma a ɓangarensu shawarwari kawai zasu iya bamu,amma yan kasar Kenya ne zasu warware wannan matsalar da kansu“