'Yan Afirka a gasar Olympics ta lokacin sanyi
Har yanzu ana daukar ’yan wasan Afirka a gasar Olympics ta lokacin sanyi a matsayin almara. Amma 'yan wasa shida daga kasashe biyar daban-daban na halartar gasar da birnin Beijing ke daukar bakunci.
Shannon Abeda (Iritiriya) - Zamiyar kankara
Iyayen Abeda sun yi gudun hijira zuwa Kanada a cikin shekarun 1980, inda Shannon ya girma kuma ya fara sha'awar wasan kwallon kankara a kasar. Amma bayan da iyayensa na ganin cewa wasan na da hadari, sai ya canza zuwa zamiyar kankara. Abeda ya wakilci Iritiriya a tseren kankara a 2011. A shekarar 2018 a Pyeongchang, shi ne dan Iritiriya na farko da ya taba shiga gasar Olympics ta lokacin sanyi.
Carlos Mäder (Ghana) - Zamiyar kankara
An haife shi a Cape Coast na kudancin Ghana, amma wani iyali na Switzerland ya karbi Mäder yana da shekaru uku. A yanzu yana da shekaru 43, kuma yana daya daga cikin tsofaffin 'yan wasan Afirka da ke halartar gasar olympics a birnin Beijing. Mäder ba shi da koci. Sakonshi shi ne: "Wasanni ba wai don cin nasara ba ne kawai, ina so in nuna wa matasa cewa idan kuna da ra'ayi, za ku iya cimma buri."
Mialitiana Clerc (Madagaska) - Zamiyar kankara
'Yar shekaru 20 da haihuwa, wani iyalin Faransa ne suka karbe ta tun tana yarinya kuma ta girma a yankin tsaunukan Alpes. A can ta koyi wasan zamiyar kankara. Burin Clerc a gasar Olympics karo na biyu bayan ta Pyeongchang a 2018: "Ina so in zama daya daga cikin gwanayen wasan kankara a duniya kuma in kasance cikin manyan 'yan wasa 40 na Beijing." Za ta kasance da Mathieu Neumuller a Beijing.
Mathieu Neumuller (Madagaska) - Tsallen kankara
Ba Mialitiana Clerc ba ce kadai za ta kare tutar Madagaska a filin wasa na Olympics a bikin bude gasar ba, amma akwai abokin wasanta Mathieu Neumuller. Kamar dai Clerc, dan shekara 18 wanda mahaifin dan Faransa kuma mahaifiyar 'yar Madagaska ce yana wasa a fannin tsallen kankara wato slalom. Burinsa shi ne ya kasance cikin gwanaye 30. Dan na gada ne, don mahaifinsa malamin wasannin kankara ne.
Samuel Ikpefan (Najeriya) - Tseren kankara
Dan wasan mai shekaru 30 ya fito ne daga yankin tsaunukan Alpes na Faransa kuma ya zama zakaran tseren Faransa tun yana matashi. A lokacin da ya kasa shiga tawagar Faransa a gasar Olympics shekaru hudu da suka wuce, ya kusa daina wasan, amma sai ya yanke shawarar shiga gasar a karkashin kasar mahaifinsa wato Najeriya. "Ina alfaharin wakiltar wata kasa ta Afirka a gasar Olympics," in ji Ikpefan.
Yassine Aouich (Maroko) - Zamniyar kankara
Aouich yana zaune ne a tsaunin Atlas a arewacin Maroko. Garinsu na Ifrane yana kan tsauni da ke da tsawon mita 1650. Akwai wuraren wasan kankara da yawa a kusa da nan, don haka mai shekaru 31 na iya samun horo a gida. Shi ne dan kasar Maroko na takwas da ya fafata a gasar Olympics ta lokacin sanyi. Dalilinsa: "Na yi wa dana alkawari cewa zan iya zuwa gasar Olympics, don haka dole ne in je."