1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan aware sun kai hari a Yuganda

November 27, 2016

Yan sanda a Yuganda sun sanar da cewar akalla jami'an tsaro 55 aka kashe hade da wasu 'yan aware a wani gumurzun da aka sha yammacin Yugandar.

https://p.dw.com/p/2TKfy
Uganda Afrika Soldaten Sicherung Demonstration
Hoto: picture-alliance/dpa/D.Kurokawa

Fadan ya afku ne a lokacin da dakarun masarautar na garin Kasese suka kai hari a kan wani ayarin 'yan sandar gwamnatin da ke yin sintiri a yanki tare da raunata wani sojin kafin daga bisannin fadan ya gama gari.Daular ta Rwenzururu ta 'yan kabilar Bakonzo  da ke tsakanin Yuganda da Jamhuriyar Demokariyyar Kwango an yi ikiranta  tun a shekara ta 1962.