1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan aware sun yi kashe-kashe a Kamaru

Mouhamadou Awal Balarabe MNA
June 20, 2021

'Yan aware da ke gwagwarmaya da makamai a Kamaru sun kashe sojoji biyu da wani ma'aikacin gwamnati daya a yankin masu magana da Ingilishi da ya shafe shekaru hudu yana fama da rikicin neman ballewa.

https://p.dw.com/p/3vEx1
Kamerun Beerdigung des achtjährigen Nsoh Macpeace in Bamenda
Hoto: Adrian Kriesch/DW

Hukumomin Kamaru sun bayyana cewar 'yan awaren Ambazoniya sun halaka dakarun gwamnati biyu a yankin kudu maso yammacin kasar da ke fama da rikicin neman ballewa. Sannan kuma sun kashe wani babban jami’in ma’aikatar tattalin arzikin Kamaru tare da yin garkuwa da wasu mutane biyar a gundumar Ndian.

Yankin da ke amfani da Ingilishi na Kamaru dai ya zama fagen fama tun tsawon shekaru hudun da suka gabata, inda rikicin neman ballewa tsakanin kungiyoyin da ke dauke da makamai da sojojin gwamnati ya ki ci ya ki cinyewa. Kungiyoyi masu zaman kansu na duniya da Majalisar Dinkin Duniya na zargin bangarorin biyu da ke gaba da juna da cin zarafin fararen hula.

Tsirarun da ke magana da Ingilishi sun zargi masu magana da Faransanci da kuma Shugaba Paul Biya da ya shafe shekaru 38 a kan kujerar mulki da mayar da su saniyar ware, lamarin da ya haifar da mummunan rikici wanda ya barnatar da rayukan mutane sama da 3,500.