'Yan bindiga sun hallaka magajin garin Belo a kasar Kamaru
May 21, 2024'Yan bindiga a Kamaru sun hallaka magajin garin Belo Ngong Innocent Ankiambom tare da mataimakinsa da kuma wani jami'i, a daidai lokacin da a ke bikin tunawa da ranar hadin kai ta kasa a ranar Litinin.
Karin bayani:Kamaru: 'Yan aware sun hana zuwa makaranta
Gwamnan yankin arewa maso yammacin kasar Adolphe Lele Lafrique, ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa tuni suka kaddamar da bincike don zakulo wadanda suka aikata wannan laifi, inda kuma ya yi kira ga al'umma da su zauna lafiya, domin hukumomi na yin iya kokarinsu na magance matsalar.
Karin bayani:Zaben shugaban kasa:Gwamnatin Kamaru ta haramta gamayyar jam'iyyu
Ko a ranar 10 ga wannan wata na Mayu sai da 'yan aware suka kashe babban kwamandan hukumar tsaro ta Jandarma da jami'ansa 4, a yankin kudu maso yammacin kasar.
Tun daga shekarar 2017 da rikicin 'yan aware ya barke zuwa yanzu, mutane sama da dubu shida ne suka rasa rayukansu a kasar ta Kamaru.