'Yan bindiga sun kai hari a Nairobi
September 21, 2013Dakarun Kenya sun ce sun yi wa 'yan bindigar da suka kai harin a cibiyar kasuwancin da ke a babban birnin ƙasar wato Nairobi ƙawanya, wanda yayi sanadiyyar hallakar aƙalla mutane 30 ciki har da ƙananan yara, ya kuma sanya mutane tserewa domin neman mafaka. An kwashi sao'i da dama ana jin harbin bindiga bayan harin da aka kai tun farko. Jami'an tsaron ƙasar dai sun kewaye babban shagon saida kayayyakin da ake kira ''Westgate Mall'', kuma 'yan sanda da sojoji sun bi kowace ƙusurwar shagon suna neman waɗanda ke da alhakin haddasa wannan ta'asa.
Bisa bayyanan kamfanin dillancin labaran Reuters, wannan harin da aka kai West gate Mall na zaman hari mafi muni tun bayan wanda ƙungiyar Alƙaida ta kai kan ofishin jakadancin Amirkan da ke Nairobi a shekarar 1998 wanda ya kai ga mutuwar mutane fiye da ɗari biyu.
Wasu kafofin yaɗa labaran Kenya sun rawaito cewa an yi garkuwa da wasu mutane amma ya zuwa wannan lokacin babu hujjojin da suka ƙarfafa wannan labari. Dama dai Ƙungiyar Al shabab da ke da mazauninta a Somaliya wadda kuma Kenya ta saba ɗorawa alhakin hare-hare irin wannan ta yi barazanar kai hari a shagon na ''Westgate Mall'' a matsayin martanin sakamakon harin da dakarun Kenya suka kai mata shekaru biyu da suka gabata.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Abdourahamane Hassane