Burkina Faso: Yan bindiga sun kashe fararen hula
May 20, 2023A kasar Burkina Faso da ke yankin Sahel, fararen hula kimanin goma sha biyu ake zargin wasu mayaka masu da'awar jihadi da kashewa a wani hari da suka kai a yankin yammacin kasar da ke iyaka da kasar Mali.
Wani ma'aikacin gwamnati da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, maharan sun zo da yawansu dauke da muggan makamai, sun afka wa kauyen mai suna Kie a daren Jumma'ar da ta gabata, in da suka yi wa kauyen kawanya kafin daga bisani sun cinna masa wuta, da wuya a iya tantance adadin mutanen da ya ce, an kashe ganin da yawa sun ji munanan rauni baya ga asarar dukiyar da aka tafka a harin.
Kazamin harin na zuwa ne, kwana guda bayan wani makamancinsa da 'yan bindiga suka kai da ya salwantar da rayuka ashirin a kasar da yanzu haka ke fada da ayyukan 'yan ta'adda.