'Yan bindiga sun halaka mutane a Zamfara
June 4, 2020Talla
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba lokacin da ake zargin maharan sun sato wasu dabbobi, al'umma kuma ta nuna tirjiya. Wani ganau ya shaida wa wakilin DW Yusuf Ibrahim Jargaba cewa har yanzu sun kasa rufe gawawwakin jama'a domin da sun je makabarta sai maharan su sake far musu. Kwamishinan tsaro a Jihar Zamfara Abubakar Justice Dauran ya ce gwamnati ta samu labarin wannan al'amari, kuma suna kan hanya zuwa yankin da lamarin ya faru.