'Yan Birtaniya sun fusata da Boris Johnson
August 29, 2019Sanarwar da Firaiministan ya yi a gaban Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu kan bukatar dakatar da ayyukan majalisar dokokin, wanda shi ma yanzu ake ta cece-kuce akai ganin yadda Sarauniyar ba tace uffan ba akan batun ya tayar da sabuwar dambarwa amma a cewar Jacob Rees-Mogg shugaban masu rinjaye a majalisar dokoki da ke goyon bayan ficewar Britaniyar, ya ce ta sami kanta cikin mawuyacin hali ganin an santa da mutunta Firaiminista.
Sarauniyar ba ta da cewa akan wannan batu, ba a taba saninta da kin amincewa da bukatar firaminista a yanayi irin wannan ba''
Sai dai ga dubban ’yan kasar da suka fantsama kan tituna don nuna fushinsu, sanarwar ta bazata karan tsaye ne ga mulkin demokradiya. Shi ma wannan dan jaridar mai suna Paul Mason, da ya shiga cikin jerin masu zanga-zangar, ya alakanta lamarin da juyin mulki kamar yadda ya saba gani a sauran kasashe a yayin gudanar da aikin jarida.
''Juyin mulki ne karara, na sha gani na kuma sha yin rahoto akai, an yi na gani a kasar Kenya, haka a Turkiya, haka ma a kasar Girka, abinda muke gani shi ne an yi awon gaba da majalisar dokoki sukutun''
Mista Johnson dai ya tsaya kai da fatan kan cewa baya son Britaniya ta fice daga kungiyar Tarayyar Turai ba tare da yarjejeniya ba, sai dai in har ya zama dole, inda kuma ya baiyana fatan yin hakan ba tare da bata lokaci ba.