1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Boko Haram sun sa mutane tserewa a jihar Borno

February 7, 2019

Hukumar kula da masu kaura ta Majalisar Dinkin Duniya ta nuna cewa 'yan Boko Haram sun sake karbe iko da wasu garuruwa a Arewa maso gabashin Najeriya, lamarin da ya sa mutane sama da budu 60 kaurace wa matsugunansu.

https://p.dw.com/p/3Cum7
Nigeria Boko Haram Anschlag in Maiduguri
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Ola

A cewar jami’in hukumar kula da masu kaura ta Majalisar Dinkin Duniya Frantz Celestin tun daga watan Nuwamban 2018, kimanin mutane dubu 59 da 200 ne suka gudu daga garuruwansu saboda hare-haren Kungiyar Boko Haram. Ya kara da cewa kokarin da gwamnati ke yin a fatattakar mayakan Boko Haram na gamuwa da cikas saboda yanayin hazo da sauran matsaloli da yankin ke fama da shi, abin da ya bai wa kungiyar damar sake kame wasu wurare daga ikon Sojojin Najeriya.

Nigeria Flüchtlinge aus Borno
Yara sun fi jin radadin gudun hijiraHoto: DW

 Hare-haren dai a cewa rahoton da hukumar ta fitar sun haifar da tsaiko ga dukkanin kungiyoyin agaji a kokarin kai kayan jin kai ga mutane da rikicin ya rutsa da su. Saboda haka ne suke gargadin da a dauki matakai na gaggawa don ceto fararen hular da ke cikin hali na tsaka mai wuya.

Sai dai a cewar wasu da suka gudu daga yankunan Arewacin jihar Borno, yawan hare-haren sun zarta adadin da hukuma ta bayar don kuwa a kullum anan samun masu fitowa kuma ba kowa ba ne yake zuwa sansanin da hukumomi ke iko da su ba. Ko da wadanda suka samu zuwa sansanonin da gwamnatin ke kula da su na fama da matsalolin rashin wurin kwanciya da kuma abinci da ruwa.

Nigeria Abuja Flüchtlinge
Jami'an agajin gaggawa na kai dauki a BornoHoto: DW/A. Kriesch

 Ko a ranar talata da ta gabata sai da wasu ‘yan gudun hijira suka yi zanga-zanga saboda kukan rashin abinci duk da dai hukumomin sun ce ba rashin abinci ne dalilin boren ‘yan gudun hijirar ba. Dubban ‘yan gudun hijira na ci gaba da kwarara zuwa Maiduguri da garuruwan da su ke da isassun matakan tsaro inda ake ci gaba da fafata yaki tsakanin mayakan Boko Haram da Sojojin Najeriya abinda ke kara jefa ayyukan jin kai cikin mawuyacin hali.