'Yan Borno sun mika koke-koke kan sojoji
September 22, 2017Gwamnatin tarayyar Najeriya ne ta kafa wannan kwamiti domin ya bi kadin korafe-korafen da 'yan Najeriya ke yi na zargin Sojoji da cin zarafinsu a kokarin yaki domin tabbatar da tsaro musamman a shiyyar Arewa maso gabashin kasar. Bayan kammala zaman karben koke a birnin tarayya Abuja, kwamitin ya je Maiduguri domin karbar koken al'ummar shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya inda kungiyoyin kare hakkin bani Adama ke ganin cewar keta hakkin mutane da ake zargin Sojojin sun yi ya fi yawa.
Iyaye da dama sun samu damar mika koke na batar 'ya'yansu da su ka yi zargin Sojojin sun kame tsawon shekaru har yanzu kuma babu labarinsu. Wasu daga cikin iyaye sun bayyana fatan za a bi musu kadi tare da sanar da su halin da 'ya'yansu ke ciki.
Farfesa Jibrin Ibrahim daya daga cikin membobin kwamitin , ya ce sun samu korafe-korafe da dama tare da ziyartar barikin Sojoji inda ake zargin ana tsare da daruruwan mutane da Sojojin suka kama.
Sai dai wasu da dama ba su samu damar mika kokensu ba saboda rashin sanin kwamitin na zaman karbar koken da kuma inda ake zaman karbar koken. Ana alakanta hakan ne da rashin fadakar da mutane sosai ta hanyoyin da za su ji duk da cewa wasu kafafen yada labarai sun sanar da cewa kwamitin zai zo amma ba a fadi rana ko wurin da za a kai koken ba.
Sai dai Kwamitin ya bada damar jama'a su mika koken na su ta hannun ma'aikatar shari'a ta jihar Borno don mika wa kwamitin. Barista Kaka Shehu wanke shi ne kwamishinan shari'a na jihar Borno ya yaba da aikin kwamitin duk da cewa kwanakin da su ka yi ba masu yawa ba ne. Kwamitin dai ya bada dama ga sauran al'ummar jihohin Arewa maso gabashin Najeriya da ba su samu damar mika kokensu ba su mika kwamitin a zaman da zai yi a sauran sassan Arewa da kudancin Najeriya.