`Yan Gambiya: ´Yan ci rani, bayi da fata na demokaradiyya
‘Yan ci rani da dama na Gambiya sun fuskanci cin zarafi a lokacin da ake tsare da su a Libiya, a yanzu sun koma gida. Yanzu da yake Gambiya na kan hanyar shiga demokaradiyya, mi ya faru ga wadanda suka tafi Turai ?
Komawa gida zuwa Gambiya
A ranar 4 ga watan Afrilu ‘yan ci rani 169 na Gambiya suka koma gida da kan su. Sun bar Gambiya sama da shekara guda, da nufin zuwa Turai. Sai dai sun tsaya a Libiya, inda da dama aka kama su aka kuma tsare su, aksari a cikin wani mummunar hali.
"Kasuwar bayi"
Kamar yadda kungiyar kaura ta duniya OIM ta shaida, ta ce’yan Gambiya an gana musu hukuba, ga rashin abinci a lokacin da ake tsare da su a Libiya. Kana wasu sun bayyana yadda aka yi kasuwar bayi da su cewar sai iyayen su ko 'yan uwa sun fanshe su sun biya kudade kafin a sake su.
Wadanda aka ceto suka dawo gida
Tare da tallafin kungiyar kaura ta OIM da gwamnatin Gambiya, wasu ‘yan Gambiyar sun samu ‘yanci a cikin wuraran da ake tsare da su a Libiya. ’Yan ci rani sun sauka a filin saukar jiragen sama na Banjul da ke a yammacin Afirka, kafin a yi musu fasfo na gaggawa, da kuma ba su wasu ‘yan kudade domin isa gida.
Tafiya mai rashin tabbas
Sun samu sun shiga jirgin ruwan a cikin wani yanayi mai hadari da nufin tsallaka tekun Baharrum. Yawancin jiragen ruwan na roba ne kana cike makil da fasinja. Sama da mutum dubu biyar ake tsammanin sun nutse a cikin ruwan tekun a shekara ta 2016.
Demokaradiyya a Gambiya
A cikin watan Disamba na shekara ta 2016 Yahya Jammeh ya sha kaye a zaben shugaban kasa a gaban dan takarar adawa Adama Barrow, Amma Jammeh ya ci gaba da dagewa a kan mulki, kafin daga bisani ya tsere bayan da dakarun kasashen yammacin Afirka suka yi barazanar korarsa. Wannan kuma shi ne mataki na farko na shigar kasar cikin tsarin demokaradiyya. Kafin a yi sauran zabubuka a cikin watan Afrilu.
Babu 'yancin samun mafaka ?
‘Yan ci ranin Gambiya wadanda suka yi Turai a yanzu suna fuskantar barazana ta kora. A yanzu ‘yan Gambiya su ne mafi yawa daga cikin ‘yan ci rani na Afirka da ke Jamus, Kuma idan a ka tabbatar kai dan asilin kasar Gambiya ne to ba za ka iya samun mafaka ba
Taki zuwa taki
Akwai babban fata na kyakyawar makoma ta demokaradiyya a Gambiya, Sai dai ba za a ia yin shuru ba a game da mulkin kama karya da ya wucce ba, tare da ganawa ‘yan adawa azaba a gidajen kurkuku. Kungiyar tarrayar Turai ta yi alkawarin bai wa kasar miliyan 75 na EURO domin goyon bayan dawowar demokaradiyya a kasar da kuma karfafa tattalin arziki.