1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Girka sun yi tir da sabon shirin tsuke bakin aljihu

Mohammad Nasiru AwalMay 9, 2016

Al'ummar kasar Girka na mayar da martani kan sabon shirin tsuke bakin aljihun gwamnati da ya tanadi karin haraji da rage kudin fansho.

https://p.dw.com/p/1IkUx
Griechenland Demonstration gegen Reformpläne
Masu zanga-zangar adawa da shirin tsuke bakin aljihu a GirkaHoto: picture alliance/dpa/O. Panagiotou

'Yan kasar Girka sun nuna rashin jin dadinsu da matakin yi wa tsarin fansho da na haraji canje-canje da 'yan majalisar dokokin kasar suka kada kuri'ar amincewa da shi, inda za a yi wa 'yan kasar karin kudaden da suke biya ga asusun inshora da fansho da kuma haraji. Spiros Michailidis wani mai kanti ne a Athens babban birnin kasar, bacin ransa ya nuna ga sabon matakin da gwamnati ke fata zai karfafa guiwar masu ba ta rance don rage matsalolin da suka yi wa kasar katutu.

"Wannan wata sabuwar shekara ce ana maimaita wani wasan kwaikwayo da aka kwashe shekaru shida ana yi. A kowace shekara ana yi mana karin haraji, ana rage kudin fansho da albashin ma'aikata. Ban san inda wannan abin zai kai mu ba."

Yanzu haka dai ministocin gungun kasashe masu amfani da kudin bai daya na Euro sun hallara a birnin Brussels inda za su tattauna kan saukaka wa kasar Girka basussukan da ke kanta.