'Yan gudun hijira sun fi miliyan 68 a 2017
June 19, 2018Talla
Rahoton ya kiyasta cewa a kowani dakika biyu akalla mutane biyu ne suka rasa muhallansu sakamakon rikicin siyasa da tashe- tashen hankula a jamhiriyar Dimukaradiyyar Kwango da Sudan ta Kudu tare da rikicin kabilanci da ya barke a Myanmar. Sai dai Majalisar Dinkin Duniya ta ce kasar Turkiyya ce ke kan gaba wajen yawan karbar 'yam gudun hijira daga Siriya.
A shekarar 2017 din kadai Turkiyya ta karbi adadin baki 'yan gudun hijira akalla miliyan Uku da rabi, yayin da kasashen Pakistan Yuganda da Lebanon da Iran da Jamus suka bi baya wajen Turkiyya wajen kasashen da 'yan gudun hijira suka fi samun mafaka.