'Yan gudun hijira sun Ƙaru dalilin Boko Haram
June 25, 2014Tashin hankalin da ke ci gaba da sanadiyyar rasa rayukan al'umma a yankin arewa maso gabashin Najeriya na sanya mutane ci gaba da ƙaurace wa matsugunansu inda wasunsu ke tsallakawa ƙasashen da ke makotaka da kasar irin su Kamaru da Chadi da Jamhuriyar Nijar, yayin da wasu ke zaune a wasu sansanonin 'yan gudun hijira da hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasar ta samar a wuraren da za a iya ɗauka a matsayin tudun na tsira.
Wani dattijo da ya zaɓi a sakaya sunansa ya shaida wa DW cewa rikcin da yankin ke fama da shi ne ya sanya shi barin inda ya fi wayo zuwa babban birnin Najeriyar Abuja don tsira da ransa. Dattijon ya ce abubuwan da ya gani da irin ta'annatin da Boko Haram din suka yi a kan idonsa su suka sanya ya ga dacewar yanke ƙauna da matsuguninsa da ke Maiduguri don neman salama.
Gabannin wannan yanayi da Jihar Borno ta shiga dai inji dattijon wanda Kirista ne, suna zaune lami lafiya da 'yan uwansa da makotansa wanda galibinsu mabiya addinin Islama ne. Dattijon ya ce wani abun tashin hankali shi ne yadda ake tursasawa matasa ɗaukar makamai don taya 'yan Boko Haram yaƙi.
To baya ga dattijon da ya ƙaurace wa jiharsa ta Borno, da ma dai nuna yadda 'Yan Boko Haram ɗin ke tilasta wa matasa shiga ƙungiyar ba da son ransu ba, Hafsat Maina Muhammad wadda 'yar jaida ce da yanzu haka ke zaman gudun hijira a Kaduna ta bayyana takaicinta dangane da wannan tsari na maida matasa mayaƙan Boko Haram.
Ta ce ''wannan batu na da takaicin gaske, Borno na cikin wani hali. Sun kashe ɗan wani abokin wasa na. Da fari sace shi suka yi ba mu sake jin ɗuriyarsa ba sai bayan shekara guda inda suka aiko mana da wasiƙa suka ce sun hallaka shi saboda ya ƙi yadda ya shiga ƙungiyar ta su. Wannan wani abu ne da ba zai taɓa ɓace min a rai ba.''
Daga ƙasa ya a iya sauraron wannan rahoto
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Abdourahamane Hassane