'Yan gudun hijiran Sudan ta Kudu na zuwa Yuganda
July 14, 2016Talla
Dubban mutane ne dai suka bar gidajensu a halin yanzu sakamakon fada na baya-bayan nan da ya barke a Juba babban birnin kasar ta Sudan ta Kudu. Mista Titus Jogo da ke zaman jami'in da ke kula da 'yan gudun hijiran na Sudan ta Kudu ya ce:
" Tun bayan da wannan tashin hankali ya soma a Sudan ta Kudu, muna samun 'yan gudun hijira 200 zuwa 250 a kowace rana, har mu ka kai muna samun kasa da 150, amma kuma yanzu sakamakon barkewar fada na birnin Juba matsalar ta dawo sabuwa."
Wata 'yar gudun hijira mai shekaru 40 da haihuwa kuma tana da 'ya'ya biyar ta ce, sojojin da ke bisa iyaka na tilasta wa mutane koma wa inda suka fifo, tare tilasta musu zubar da kayayakinsu kafin su ketara a kasar ta Yuganda.