1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira 139 na Moria iso Jamus

Abdullahi Tanko Bala
September 30, 2020

Tagawar yan gudun hijira yara kananan da ke fama da matsaloli na rashin lafiya tare da iyayensu sun sauka Jamus a matakin farko na sake tsugunar da yan gudun hijirar bayan gobarar da ta kone sansanin Moria na kasar Girka

https://p.dw.com/p/3jEqX
Deutschland Migranten aus Moria landen in Hannover
Hoto: Julian Stratenschulte/dpa/picture-alliance

Jirgin farko dauke da 'yan gudun hijira 139 daga Girka ya iso Jamus ciki har da yara kanana da aka barsu suna watangaririya bayan iftila'in gobara da ta kone sansanin 'yan gudun hijira na Moria da ke tsibirin Lesbos.

Jamus ta amince za ta karbi yaran da basa tare da iyayensu wadanda aka kai su wani sansani a cikin Girka bayan aukuwar gobarar.

Yara 51 daga sansanin na Moria da aka dauko sun sauka a filin jirgin saman Hannover a cewar ma'aikatar cikin gida ta Jamus 

A baya bayan nan gwamnatin Jamus ta yi alkawarin karbar 'yan gudun hijira 1,533 daga tsibirin Girka.