1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Habasha na dandana kuda a hannun gwamnati

Lateefa Mustapha Ja'afar M. Ahiwa
May 31, 2023

Miliyoyin mutane a Habasha na cikin talauci tun bayan rantsar da Firaminista Abiy Ahmed shekaru biyar din da suka gabata, kuma babu wani wanda ya isa fitowa domin sukar gwamnati.

https://p.dw.com/p/4S1EF
Hoto: Facebook.com/Office PM Ethiopia

Mutane da dama a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha na cikin matukar talauci, bayan rantsar da Firaminista Abiy Ahmed shekaru biyar din da suka gabata. Sai dai babu wanda ya isa ya fito fili domin sukar gwamnati. An ma rufe kafafen sada zumunta na zamani a Habasha. Masu kudi ne kawai ke iya samun labaran da ba a tantance ba.

Cikin dan kankanin lokaci ne dai, yawan al'ummar Habasha da ke yankin gabashin Afirka ya karu da kusan rabi. Sama da mutane miliyan 120 ne a yanzu ke zaune cikin kasar, abin da ya sanya ta zama kasa mafi yawan al'umma a nahiyar bayan Najeriya. Mata da dama sun hayayyafa da karancin shekaru saboda babu cikakken ilimi ko wayar da kai dangane da batu na tsarin iyali. A yanzu babban birnin kasar ya yi cikar kwari. Kuma kananan 'yan kasuwa da dama a Habashar na fama da karancin kudi.

A shekarun da suka gaabata dai, Habasha ta kasance kasar da ke kan gaba cikin kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa a duniya da sama da kaso 10 cikin 100. Sai dai tun bayan da yaki ya barke a yankin Tigray na kasar, al'amura suka rincabe. Al'ummomin kasa-da-kasa sun daina kai kudinsu na agaji, yanayin al'ummar kasar ya tabarbare matuka. Farashin kaya ya hauhawa da sama da kaso 30, yayin da kudin kayan abinci ya hau da sama da kaso 40 cikin 100.

Symbolbild Armut in Afrika
Hoto: picture-alliance/blickwinkel/McPHOTO/S. Wolf-Feix

Da dama dai daga al'ummar Habasha na cewa ba su da wani fata na rayuwa za ta inganta nan ba da jimawa ba, mafi akasari ma suna da fargaba tare da tsoron su bayyana halin da suke ciki. Shekaru biyar din da suka gabata dai, ana daukar Firaminista Abiy Ahmed a matsayin dan siyasa mai sadaukar da kai. Ko bayan da ya yi rantsuwar kama aiki ma, ya sha alwashin bai wa mutane karin 'yanci. Sai dai bayan jin dadi na wani dan lokaci, fata ya kauce a cewar Befekadu Hailu na cibiyar kare 'yancin dan Adam da dimukuradiyya a Habasha.

Rahotanni dai sun nunar da cewa Firaminista Abiy na rayuwa cikin daula, inda yake gina babban rukunin gidaje a saman wani tsauni a babban birnin kasar da ake zargin akwai filin wasan kwallon kwando da na golf a ciki. A karshen shekara ta 2020, shekara guda bayan da aka ba shi kyautar zaman lafiya ta Nobel, Firaminista Abiy Ahmed ya tura dakarunsa zuwa arewacin kasar. Hakan ya ta'azzara rikicin da ake yi da 'yan tawayen yankin Tigray, abin da ya haifar da asarar rayukan kimanin mutane dubu 800 cikin shekaru biyu. Dubban mutane sun kasance cikin yunwa, abin da ya janyo wa Abiy kiraye-kirayen kawo karshen yakin. Wannan suka da take sha dai, ya sanya gwamnatin Abiy kokarin tursasa al'ummar kasar.