'Yan italiya da aka sace sun koma gida
January 16, 2015Talla
Ministan harkokin wajen Italiya din Paolo Gentiloni da wasu mukarraban gwamnati ne suka marabci Greta Ramelli da takwararta Vanessa Marzullo a wani filin jirgin sama na sojin da ke kusa birnin Rome da sanyin safiyar wannan Juma'ar
Masu aiko da rahotanni suka ce saukarsu ke da wuya aka wuce da su asibiti don duba lafiyar inda daga bisani za su gana da masu gabatar da kara na kasar kan harkokin da suka danganci yaki da ta'addanci.
A karshen watan Yulin shekarar da ta gabata ne dai aka sace wadannan mata a birnin Aleppo na kasar Siriya kwanaki uku kacal bayan isarsu kasar daga kasar Turkiyya da ke makotaka da Siriyan.