1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Afghanistan: Mahara sun halaka mata 'yan jarida

Ramatu Garba Baba
March 2, 2021

Mata 'yan jarida uku ne suka rasa rayukansu a sakamakon wasu hare-hare da 'yan bindiga suka kai a wannan Talatar a kasar Afghanistan.

https://p.dw.com/p/3q7Tb
Afghanistan Frauen Radio
Aikin jarida na fuskantar kalubale a AfghanistanHoto: picture alliance/AP Photo/N. Rahim

'Yan jaridan sun gamu da ajalinsu ne bayan wasu hare-hare da maharan suka kai a yankin gabashin kasar Afghanistan. Shahnaz da Sadia na aiki ne a gidan rediyo a yayin da Mursal Wahidi ke aiki da wata kafar talabijin da ke garin Jalalabad. Maharan sun bude musu wuta a lokuta dabam-dabam a yayin da suke kan hanyarsu ta koma wa gida bayan kamalla aiki.

Matan duk sun yi suna, bisa kwarewarsu da kuma jajircewa a aikin jarida. Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin a kasar ta Afghanstan, da ta kasance daya daga cikin kasashen duniya, mafi hadari a gudanar da aikin jarida a sanadiyar barazanar aiyukan masu tayar da kayar baya. Zabihullah Mujahid, wani mai magana da yawun Kungiyar Talliban da tayi kaurin suna a aiyukan ta'addanci, ya nesanta kungiyar da hannu a harin. Shugaba Ashraf Ghani, a na shi bangaren yayi Allah-wadai da harin da ya ce ya sabawa duk wani koyarwa ta addinin Islama.