'Yan kasashen waje a gasar Bundesliga
Akwai fitattun 'yan kwallon kasashen waje masu yawa, da ke taka leda a gasar Bundesliga. Wasu na bari da wuri wasu kuma na dadewa, kamar Claudio Pizarro ko Naldo ko kuma Robert Lewandowski. Sun jima a cikin gasar.
Hasan Salihamidzic ya buga wasanni 321
A wasansa na farko a Bundesliga ya bayar da mamaki, ya fara bugawa kungiyar Hamburg a shekara da 1995. A 1992 yayin da ake yakin Bosniya ne iyayensa suka turo shi wajen wani dan uwansu a Hamburg, a lokacin yana dan shekaru 15. A 1998 ya koma kafin ya koma Juventus, kana a 2012 ya yi ritaya lokacin yana kungiyar Wolfsburg. Amma har yanzu Salihamidzic daraktan wasanni ne a FC Bayern.
Dede ya buga wasanni 322
Zai wahala a samu dan wasan da ya fi tashe a tsakanin magoya bayan Dortmund kamar dan Brazil din mai lamba 17. Daga 1998 zuwa 2011 ya buga wasa a barin hagu, inda ya lashe kofin kalubale na Jamus a kungiya daya tilo da ya yi wasa tun daga 2002 zuwa 2011. Ya bugawa kasarsa Brazil wasa sau daya, inda aka rinka kiran Leonardo de Deus Santos da Bajamushe saboda zuwa a kan lokaci.
Ole Björnmose ya buga wasanni 323
Dan wasan gaban dan ksar Denmark, ya yi wasa na tsawon shekru 11 a Bundesliga. Bayan kakar wasanni biyar a Werder Bremen, kafin ya koma Hamburg tare da lashe kofin kalubale na Jamus a 1976. A 1977 ya lashe kofin kalubale na Turai, kafin ya koma kasarsa Denmark. Har zuwa shekara ta 2008 shekaru biyu bayan rasuwarsa, Björnmose ya kasance dan wasan kasar waje da ya fi taka leda a Bundesliga.
Rafinha ya buga wasanni 332
Dan Brazil din (dama) ya dauki hankalin kungiyoyin Turai a gasar 'yan kasa da shekaru 20 da ak yi a Holland, kuma ya dawo kungiyar FC Schalke a shekarar. Bayan shekaru biyar, mai horas da 'yan wasa Felix Magath ya sallame shi ya koma Italiya. Bayan shekara guda ya dawo Bundesliga. Ya lashe gasar Bundesliga sau bakwai a Bayern da kofin kalubale sau hudu da kuma kofin zakarun Turai a 2013.
Lukasz Piszczek ya buga wasanni 332
Ya kwashe shekaru a matsayin dan wasan baya na Borussia Dortmund. Daga 2010 zuwa 2021 Lukasz Piszczek ya yi taka leda a BVB. Amma wasanninsa 68 na farko a Bundesliga, ya buga su ne a kungiyar Hertha Berlin. Bayan Hertha Berlin din ta sauka zuwa Bundesliga rukuni na biyu dan kasar Poland din ya koma Dortmund, inda Piszczek ya lashe gasar Bundesliga sau biyu da kuma kofin kalubale na Jamus sau uku.
Ze Roberto ya buga wasanni 336
A 1998 Ze Roberto wanda ya koma Real Madrid daga Flamengo Rio de Janeiro ya kaura zuwa Bayer Leverkusen. A 2002 kuma ya daga zuwa Bayern, inda ya lashe kofi guda. A 2009 lokacin tuni ya cika shekaru 35, ya samu kwantiragin shekaru biyu da Hamburg. A 2011 Ze Roberto ya bar Jamus, sai dai ya ci gaba da sharafinsa a harkar tamaula har ya kusa shekaru 43 a duniya.
Naldo ya buga wasanni 358
Kungiyar farko da Ronaldo Aparecido Rodrigues ko Naldo ya fara buga wasa daga 2005, ita ce SV Werder Bremen. Daga bisani dan wasan bayan, ya buga wasa a Wolfsburg da Schalke. Ga magoya bayan Schalke dan Brazil din gwarzo ne, saboda ya farke wasansu da Dortmund hudu da hudu dab da tashi bayan Dortmund ta ci hudu da nema. Naldo ya lashe kofin kalubalen Jamus sau biyu, daya a Bremen daya a Wolfsburg.
Makoto Hasebe ya buga wasanni 366
Dan kasar Japan din guda ne cikin fitattun 'yan wasa da ba su taba yin wasa a Bayern ko Dortmund ba, amma ya lashe gasar Bundeslig rukuni na biyu a 2009 lokacin yana wasa a Wolfsburg. A 2014 ya koma Nürnberg kafin shekara guda baya ya koma Eintracht Frankfurt, inda a 2018 ya lashe kofin kalubale na Jamus kuma a yanzu haka shi ne kyaftin din kungiyar.
Daniel Caligiuri ya buga wasanni 371
Dan wasan tsakiyar, na da fasfo din kasashen Italiya da Jamus. Sai dai an haifi Caligiuri kuma ya taso a kudancin Jamus. A 2007 ya fara buga wasannin bundesliga a Freiburg. Bayan ya taka leda a Wolfsburg da Schalke, a yanzu mai shekaru 34 a duniya ya koma kungiyar Augsburg da ke zaman kungiya ta hudu da ya buga wasa a Bundesliga.
Robert Lewandowski ya buga wasanni 384
Dan kasar Poland din, ya kafa tarihi irin wanda Gerd Müller guda daga cikin mafiya cin kwallo a tarihin Bundesliga. A 2010 Lewandowski ya dawo Borussia Dortmund daga Posen. Bayan shekaru hudu ya koma Bayern, inda Lewandowski ya kafa tarihi ba kawai domin yawan kwallayin da ya ci ba. A lokacin bazara na shekara ta 2022 da ta gabata ne, ya sauya sheka zuwa FC Barcelona.
Claudio Pizarro ya buga wasanni 490
Tsakanin shekarar 1999 zuwa 2020, dan kasar Peru din ya taka leda a Bremen kafin ya koma Bayern Munich daga nan kuma ya koma Cologne. Ya zura kwallaye 197 a Bundesliga. Pizarro wanda ya koma SV Werder har sau biyar kafin ya yi ritaya daga kwallo a bazarar 2020, ya lashe kofin Bundesliga sau shida da kuma na kalubale sau shida. Yana Bayern, ya lashe daya cikin kofunan sau hudu dayan kuma sau uku.