'Yan Kenya na hankoron samun canjin gwamnati
August 7, 2017A daidai lokacin da aski ya kai gaban goshi dangane da zaben kasar Kenya inda ake kankankan tsakanin 'yan takarar neman shugabancin kasar, 'yan kasar ta Kenya da za su jefa kuri'a a zaben na ranar Talata, suna fatan samun canjin gwamnati.
Kafin su iya kada kuri'a dole sai wasu 'yan kasar sun je yankunan da suka yi rajista. Wasu sun damu cewa tashin hankali ka iya barkewa a lokacin zaben suna masu yin tuni da rikicin da ya faru bayan zaben 2007.
Wasu daga cikin 'yan kasar na nuna rashin gamsuwarsu da mulkin gwamnatin da ke ci, kamar yadda wannan mutumin mazaunin birnin Nairobi ya nunar.
"Muna sa ran samun canjin da muke bukata. Komai ya yi tsada, rayuwa ta yi wahala. Sun kasa cika alkawuran da suka dauka. Saboda haka muna bukatar canji, muna bukatar sabbin jini wadanda za su ba mu sabuwar alkibla, amma ba irin wadda muke kanta ba yanzu."
Hasashe dai na nuni da cewa ana kankanta tsakanin shugaba mai ci Uhuru Kenyatta da babban abokin adawa Raila Odinga.