1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Najeriya ba su yarda an murkushe ta'addanci ba

January 11, 2023

Al'ummar arewa maso gabashin Najeriya na martani bayan ikirarin Shugaba Buhari na cewa gwamnatinsa ta murkushe kungiyoyin ta'adda irin su Boko Haram a shiyyar.

https://p.dw.com/p/4M1Eb
Hoto: Nigeria Prasidential Villa

Shugaba Muhammadu ya bayyana cewa gwamnatin da ya ke jagoranta ta murkushe mayakan Boko Haram da ire-iren su a shiyyar, a lokacin wata ziyarar yakin neman zaben 'yan takarar jam'iyyar APC a garin Damaturu babban birnin jihar Yobe. Da ma dai gwamnatin Najeriya ta sha alwashin cewa za ta kawo kashen matsalolin tsaro da ake alakantawa da Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriyar zuwa karshen shekarar da ta gabata kamar yadda shugaban kasa da jami'ai suka bayyana.

Haka kuma Shugaba Buhari ya sha fadi yana kuma nanatawa cewar ba zai gadar da matsalar tsaro ga shugaban da zai gaje shi, kamar yadda shi din ya gaji matsalar ba. Wannan ya sa shugaban ya bayyana wa dandazon magoya bayan jam'iyyar APC a Damaturu, cewa shi fa ya cika nashi alkawarin na kawo karshen matsalar tsaro ta Boko Haram a shiyyar. Wannan ma kuma shi ne matsayin gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni wanda ya ce a baya kusan kashi saba'in cikin dari na jihar na hannun mayakan Boko Haram.

Nigeria Zwangsabtreibungen, Soldaten mit Boko Haram Flagge
Hoto: REUTERS

Sai dai al'ummar shiyyar arewa maso gabashin Najeriya na bayyana ra'ayoyin su mabanbata kan wannan ikirari na shugaba Buhari na kawo karshen Boko Haram. Yayin da wasu ke goyon bayan maganar shugaban kasar, wasu kuma na cewa ba za a iya a'a ba, sai dai an samu sauki domin ba a iya murkushe su gaba daya ba.

Sale Bakuro Baraden Tikau na jihar Yobe ya na cikin masu bayyana gamsuwa da cewa an samu gagarumar nasara a yaki da Boko Haram. Shi kuma Dr Lawal Jafar Tahir na jami'ar jihar Yobe da ke Damaturu cewa ya yi an samu saui matsalat tsaro amma dai da sauran Rina a kaba.

Amma akwai wadanda ke ganin har yanzu mayakan na Boko Haram na nan ba a ci karfinsu ba don kuwa akwai wuraren da suke iko da su har ya zuwa wannan lokaci. Salisu Rabi'u wani mazaunin Maiduguri ne fadar gwamnatin jihar Borno garain da aka faro wanann rikici na Boko Haram.

Masu fashin baki kan harkokin yau da kullum dai na ganin an samu sauki sai dai ba iya murkushe kungiyoyin Boko Haram da na ISWAP baki daya don ko a kwanakin baya kakakin majalisar dokokin jihar Borno ya bayyana cewa Boko Haram ne ke iko da da wasu kananan hukumomi biyu a jihar.