1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

´Yan sanda a Birtaniya sun kai samame a gabashin birnin London

September 2, 2006
https://p.dw.com/p/Bukl
An kame mutane 14 a wani samame na yaki da ´yan ta´adda da ´yan sandan Birtaniya suka kai cikin wani gidan cin abinci na ´yan China dake gabashin birnin London. A halin yanzu ana tsare da mutane a karkashin dokar yaki da ta´addanci. Kame kamen dai sun biyo bayan watanni masu yawa da aka shafe ana sa ido akan harkokin mutane. Wani mai magana da yawon ´yan sandan birnin London ya ce an kai samamen ne a jiya da daddare da kuma yau da safe. To amma kame kamen ba su da alaka da kame wasu mutane fiye da 20 da ake zargi da shirye shiryen ta da bama-bamai a cikin jiragen sama da suka nufi Amirka ta hanyar amfani da bama-baman da aka harhada da sinadari masu ruwa-ruwa. Shugaban hukumar ´yan sandan Birtaniya Peter Clarke ya fadawa manema labarai cewa jami´an tsaro sun kuma gudanar da binbcike cikin wata makarantar Islamiya dake gabashin Birtaniya.