'yan sanda a Kenya sun ce zasu hana gangamin adawa na mako mai zuwa
January 11, 2008Talla
Bayan sanarda da shirin gudanar da gangami da jam’yar adawa a Kenya tayi nan take rundunar ‘yan sanda ta sanarda cewa ba zata amince a gudanar da wannan gangami ba. Yan sanda dai a baya sun dakatar da yunkuri na baya da ‘yan adawa sukayi na yin maci cikin birnin Nairobi domin nuna adawarsu game da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa. Rukicin da ya biyo bayan sake zaɓen shugaba Mwai kibaki ya halaka mutane 600 tare da wasu 250,000 da suka tsere daga gidajensu. A halinda ake ciki kuma a mako mai zuwa tsohon sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan zai fara na shi ƙoƙari na shiga tsakani a mako mai zuwa bayan rashin samun nasarar shugaban Ƙungiyar Taraiyar Afrika kuma shugaban Ghana John Kufour.