'Yan sanda a Kenya sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye a kan masu zanga-zanga
July 7, 2014A birane da dama na kasar Kenya 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye a kan masu zanga-zangar nuna kyamar gwamnati. Madugun 'yan adawa Raila Odinga ya kira zanga-zangar a babban birnin kasar Nairobi a wannan Litinin. Da ma dai 7 ga watan Yuli na zama ranar boren jama'a a Kenya. A karshen mako mutane da dama sun rasu sakamakon hare-hare a wurare da dama na gabar tekun kasar. Kungiyar al-Shabaab ta kasar Somaliya ta dauki alhakin kai hare-haren. Amma 'yan sanda da gwamnati na zargin kungiyoyin 'yan banga a yankin da hannu a tashe-tashen hankulan. Wasu tashe-tashen hankulan da aka samu a baya ma, gwamnati ta dora alhakinsu kan kungiyoyin siyasa masu gaba da juna, duk kuwa da ikirarin da al-Shabaab ta yi cewa ita ce ke da hannu ciki.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe