1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sanda sun gano maharin London na uku

Abdul-raheem Hassan
June 6, 2017

Hukumar 'yan sandan Birtaniya, ta tabbatar da sunan Youssef Zanghba a matsayin mutum na uku cikin maharan da suka kai harin kisa da motar daukar kaya kan jama'a a gadar London a karshen mako.

https://p.dw.com/p/2eCAf
London - Polizei auf London Bridge
Hoto: Reuters/P. Nicholls

'Yan sandan sun ce bincike ya nuna matashin mai shekaru 22 na da ruwa biyu na kasashen Italiya da Maroko. Rahotanni sun tabbatar da cewa jami'an tsaro a filin sauka da tashin jiragen sama na Italiya sun tsare maharin a bara, a yunkurinsa na zuwa Turkiyya dan tsallakawa Gabas ta Tsakiya da nufin hadewa da kungiyar IS.

Hukumar leken asiri ta Birtaniya, ta riga ta bayyana sunayen Khuram Butt dan kasar Pakistan da Rachid Redouane dan yankin Barking a gabashin London cikin mutane biyu da suka kai harin na ranar Asabar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. An kuma sallami mutane 12 da aka tsare bisa zargin alaka da harin.