1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfghanistan

'Yan Taliban sun gindaya sharuddan halartar taron MDD

February 17, 2024

Gwamnatin Taliban ta gindaya sharudda a game da halartar zaman taron tattaunawa karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya kan makomar Afghanistan.

https://p.dw.com/p/4cXIo
'Yan Taliban sun gindaya sharuddan halartar taron MDD
'Yan Taliban sun gindaya sharuddan halartar taron MDDHoto: AHMAD SAHEL ARMAN/AFP/Getty Images

Makasudin taron na kwanaki biyu da aka shirya gudanarwa a ranar Lahadi 18.02.2024 a birnin Doha na kasar Qatar shine share fagen dawo da alaka tsakanin Afghanistan da kasashen duniya bayan da aka mayar da kasar saniyar ware tun lokacin zuwan 'yan Taliban masu kaifin kishin Islama kan madafun iko.

Daga cikin sharuddan, 'yan Taliban sun bukaci cewa su kadai za su wakilci kasar Afghanistan a matsayin halastatun hukumomi a taron na Doha, sannan kuma suna bukatar ganawa a asirce da sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.

Tun bayan dawowar 'yan Taliban kan mulkin a shekarar 2021 kasashen Yamma da kungiyoyin kasa-kasa sun ki amincewa da su a matsayin halastattun hukumomin Afghanistan sakamakon shinfida dokoki da suka sabawa hakkin dan Adam.