'Yan tawaye a Siriya sun cafke wani gwamna
March 5, 2013Talla
Masu fafutuka a Siriya sun ce 'yan tawaye sun sace gwamnan lardin arewacin Raqqa a daidai lokacin da dakarun 'yan adawa ke ƙoƙarin murƙushe tsirarun magoya bayan shugaban ƙasar da suka rage a babban birnin lardin.
Ƙungiyar kare haƙƙin bil adamar da ke da mazauninta a Birtaniya, wacce kuma ke sanya ido a Siriyar ta ce 'yan tawayen sun cafke Hassan Jalili ne bayan da aka kwana ana ɗauki ba daɗi a gaban gidansa.
Jalili shine jami'in gwamnati mafi girma da ya faɗa hannun 'yan tawayen tun ɓarkewar rikicin na kusan shekaru biyu yanzu, kuma idan har yan tawayen suka anshe jagorancin lardin Raqqa zai zama karon farko da wani lardi zai kasance ɗungun a hannun 'yan tawaye.
Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Umaru Aliyu