1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawaye sun bijire wa sulhu a Kwango

November 25, 2022

'Yan tawaye Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango sun ce babu ruwansu da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a baya-bayan nan tare da nuna bukatar tattaunawa da gwamnati.

https://p.dw.com/p/4K5L9
Dan tawayen Kwango rike da makaminsa
Hoto: Benjamin Kasembe/DW

Kungiyar tawayen M23 da ke fada da dakarun gwamnatin Jamhuriyar dimukuradiyyar Kwangon tare da zafafa kai hare-hare a gabashin kasar, ta yi ikrarin cewa yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a Angola ba ta shafeta ba saboda kasancewar an yi zama ne ba tare da wani wakilcin kungiyar ba. A ranar Larabar da ta gabata ce dai tawagar kasashen Kwango da Ruwanda da Angola da kuma Burundi, suka gudanar da wani karamin taron koli inda suka sanya hannu kan yarjejeniyar dakatar da bude wuta da ake sa ran ta fara aiki da yammacin Juma'a, inda suka bukaci 'yan tawayen da su janye daga yankunan da suka mamaye ko kuma su fuskanci farmaki daga dakarun hadaka na gabashin Afirka.

Da fari dai, wasu na ganin yarjejeniyar ka iya zama wani tubali na samun masalaha a tsakanin bangarorin biyu. Sai dai masu nazari kan rikicin kasa-da-kasa na cewa duk wanda ya sayi rariya dai ya san za ta zubar da ruwa. A ranar Alhamis, daruruwan mutane suka gudanar da zanga-zanga a birnin Goma da ke gabashin Kwangon don nuna adawa da yarjejeniyar, saboda a cewarsu an dade ana gafara sa, amma ba a ga kaho ba; kuma yarjejeniyar da aka cimma ba za ta dakatar da zargin da suke yi wa kasar Ruwanda ba. Kwangon dai na zargin makwabciyarta Ruwanda da mara wa 'yan tawayen baya, zargin da gwamnatin Kigali ta musanta.

RDC Jugendliche in der Armee in Goma
Hoto: Zanem Nety Zaidi/DW

Masu boren sun ce, wannan yarjejeniya ba ta shafe su ba kai tsaye saboda a cewarsu an sha gudanar da irin wadannan tarukan a baya ba tare da haka ta cimma ruwa ba, kuma burinsu shi ne a samar da zaman lafiya mai dorewa da ma tabbatar da tsaron al'umma. Tuni wasu suka fara mika bukata kan cewa kasashen Ruwanda da kuma Yuganda su janye dakarunsu daga Kwango. Mayakan M23 dai sun kwace ikon yankuna da dama a garin Goma da ke Lardin Kivu na gabashin Kasar. Dubban mutane ne dai suka rasa matsugunnasu yayin da suka tserewa yankin da ke fuskantan hare-haren 'yan tawayen.