'Yan wasan Kenya da shan kwayoyi a Olympic
August 26, 2015Talla
Wasu 'yan kasar Kenya da suka shiga gasar guje-guje da ake yi cikin wasannin Olympic a kasar China sun karbi takardar da ke haramta musu shiga irin wannan wasani a nan gaba.
Koki Manunga da Joyce Zakary sun karbi wannan takarda a ranar Laraban nan bayan da kungiyar kasa da kasa da ke shirya wasannin na motsa jiki IAAF ta gano cewa suna ta'ammali da kwayoyi masu kara kuzari.
A cewar jawabin da hukumar ta IAAF ta fitar 'yan wasan na Kenya masu shiga gasar guje-guje an gano mu'ammalarsu da magunguna masu kara kuzari bayan gwajin da aka yi musu a otel din birnin Beijing a ranakun 20 ga watan Agusta da ranar 21 ga watan na Agusta.