1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Zimbabuwe sun fita da yawa don kada kuri'a

Mohammad Nasiru Awal SB
July 30, 2018

Tun da sanyin safiyar wannan Litinin aka fara samun dogayen layuka a tashoshin zabe da takararsa ta fi zafi tsakanin shugaba mai ci Mnangagwa na ZANU-PF da Chamisa na MDC.

https://p.dw.com/p/32JjR
Simbabwe Präsidentenwahl
Hoto: Reuters/M. Hutchings

A zabukan farko a Zimbabuwe tun bayan murabus din tsohon shugaban kasa Robert Mugabe a bara, an samu yawan masu zabe da suka fita kada kuri'a.

Rahotanni sun ce tun da sanyin safiyar wannan Litinin aka fara samun dogayen layuka a tashoshin zabe da takararsa za ta fi zafi tsakanin shugaba mai ci Emmerson Mnangagwa na jam'iyyar ZANU-PF da Nelson Chamisa na jam'iyyar adawa ta MDC.

A lokacin da ya kada kuri'arsa a yankin Kwekwe, Shugaba Mnangagwa ya yaba da yadda zaben ke gudana cikin kwanciyar hankali da lumana.

"Ina farin cikin yadda yakin neman zabe ya gudana cikin lumana da kuma yadda zaben na yau ke gudana cikin kwanciyar hankali. Ba ni da shakku karshen shirin zaben gaba daya zai kasance cikin kwanciyar hankali da lumana."

Shi ma dan takarar babbar jam'iyyar adawa ta MDC, Nelson Chamisa bayan ya kada kuri'arsa cewa ya yi nasara tabbatacciya ce a garesu.

"Ba mu da shakku matukar an yi gaskiya da adalci a zaben, to nasara tana ga al'umma. Al'umma ta yi magana, a baiyane yake cewa zabe ne na nasara, zabe ne na 'yanci, zabe ne na dimukaradiyya, zabe ne kuma na wata sabuwar Zimbabuwe."

Mutane kimanin miliyan 5.5 ne aka yiwa rajistar zabe a kasar ta Zimbabuwe da ke neman sauyi bayan tattalin arzikinta da harkokin siyasa sun ruguje sakamakon mulkin kusan shekaru 40 na Robert Mugabe.