1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan ƙasar Somaliya dake hijira na fuskantar barazana daga Al-Shabab

November 11, 2011

Duk da cewar sun yi ƙaura daga ƙasarsu sakamakon yaƙin basasar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, 'yan ƙasar Somaliya ba su tsira daga ta'asar Al-Shabab ba

https://p.dw.com/p/139OZ
Harin ta'addancin Al-Shabab da ya rutsa da farar hulaHoto: picture alliance/dpa

A wannan makon dai babban abin da ya fi ɗaukar hankalin jaridun na Jamus dangane da al'amuran nahiyarmu ta Afirka shi ne halin da ake ciki a ƙasar Laberiya bayan zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar, wanda kuma 'yan hamayya suka yi kiran ƙaurace masa. A cikin nata rahoton jaridar Die Welt cewa tayi:

"Duk da yabawar da 'yan sa ido na ƙasa da ƙasa suka yi da zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasa a Laberiya, wanda suka ce an gudanar da shi akan addalci da kwanciyar hankali, amma 'yan hamayya sun yi kiran ƙaurace wa zagaye na biyu na zaɓen. Hakan ta sanya yawan waɗanda suka fita kaɗa ƙuri'a bai taka kara ya karya ba. Sai dai kuma ita kanta gwamnatin shugaba Ellen Johnson Sirleaf, ana zarginta da taɓargaza ta cin hanci da almundahana. Wani abin lura ma shi ne kasancewar dab da zaɓen na raba gardama, gwamnatin ta ba da umarnin rufe wasu tashishin telabijin guda biyu da kuma gidajen rediyo uku saboda yaba wa abokin hamayyarta Tubman da suke yi a rahotanninsu. Wannan matakin kuwa ba shakka yayi daura da manufofin demokraɗiyya."

Liberia Wahlen in Monrovia Winston Tubman
Babban ɗan hamayyar Liberia Winston TubmanHoto: DW

'Yan gudun hijirar Somaliya dake ƙetare sun shiga hali na zaman ɗarɗar a game da karnukan farautar ƙungiyar Al-Shabab, musamman ma a Nairobin Kenya, inda da yawa daga 'yan gudun hijirar Somaliyar, da suka ƙaurace wa ƙasar sakamakon yaƙin basasarta da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, suke da zama, kamar yadda jaridar Die Tageszeitung ta rawaito ta kuma ƙara da cewar:

"A haƙiƙa ma dai tuni yaƙin basasar Somaliyar ta rutsa da ƙasar Kenya. Domin kuwa tun bayan da ƙasar ta tura sojojinta zuwa Somaliya su ma ƙungiyar Al-Shabab suka lashi takobin sanya ƙafar wando ɗaya da Kenyar. Akwai ma rahotannin dake nuna cewar ƙungiyar ta Al-Shabab, ba kawai Somaliyawan dake Kenxya ne take ɗauka aikin soja ba, har ma da wasu ƙabilu na ƙasar ta Kenya, saboda matsalar rashin aikin yi da tayi wa ƙasar katutu kuma mutane ba su buƙatar wata aƙida ta addini wajen neman abin sakawa bakin salati."

Gründe für Migration Krieg Somalia Muslime ethnische Konflikte Verteibung
Ƙungiyar Al-Shabab na ɗaukar dakarun mayaka da ba 'yan kasar somaliya ba a ƙetareHoto: AP

Tun bayan da kudancin Sudan ta samu 'yancin kanta watan yulin da ya wuce, Amirka ta fara mayar da hankali kan arziƙin man fetir da Allah Ya fuwace wa yankin da kuma fafutukar gina hanyoyin sadarwarsa. Wannan rahoton jaridar Der Freitag ce ta rawaito shi, ta kuma kara da cewar:

"Sai daikuma a inda take ƙasa tana dabo shi ne kasancewar har yau ƙura ba ta lafa a rikicin da aka daɗe ana fama da shi tsakanin arewaci da kudancin Sudan ba. Domin kuwa ko da yake ana zargin fadar mulki ta Khartum da amfani da ƙarfin bindiga a yankuna Abyei da kudancin Kordofan, amma fa su ma dakarun kudancin Sudan, kamar yadda hotunan da aka ɗauka ta taurarin ɗan-Adam suka nunar, a nasu ɓangaren su kan kai farmaki kan sojan gwamnatin Sudan."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi