Hakkin bil Adama na samun Ilimi
June 23, 2012Shin gamayyar ƙasa da ƙasa ta cimma muradinta na kare hakkin bil Adama na samun ilimi ? Wannan ita ce tambayar da taron kafafen yada labaru na kasa da kasa da DW za ta gudanar daga ranar 25-27 ga watan Yuni zai yi kokarin ba da amasarta
"Mu ba mu da wata kwarewa ta aiki saboda haka muna bukatar a bamu ilimi." Wadannan sune kalaman da daliban kasar Spaniya suka rubuta akan kwalaye yayin wata zanga-zanga da suka gudanar a farkon shekarar 2012 domin nuna adawa da shirin sayar da manyan makarantun gwamnati. Hakan dai wani kira ne ga gwammati da ta tabbatar da hakkin bil Adama na samun ilimi. Claudia Lohrenscheit, jami'ar cibiyar nazarin hakkokin bil Adama ta Jamus ta ce:
Gwamnatoci na bukatar sauke nauyin da ya rataya a wuyansu
"Ba al'uma damar zuwa makaranta da kuma samun ilimi alhaki ne da ya rataya a wuyan gwamnatoci ba tare da alakanta hakan da yanayin tattalin arziki ba. Wannan dai abu ne da gwamnatoci suka tabbatar a cikin shelar kare hakkin bil Adama da ta hada da samun ilimi."
Ba kasashe matalauta ne kadai ke fuskantar matsala wajen tabbatar da hakkin bil Adama na samun ilimi ba, hatta kasashen yamma masu arzikin masana'antu su kuma suna fuskabtar matsala a wannan fannin. Kamar dai yadda hukumar kula da cinikayya da raya kasashe ta MDD, UNCTAD ta nunar a cikin wani rahoton da ta wallafa a baya-bayan nan, manufar dunkulewar duniya a wuri daya da ke da alaka da aikin kudi ya samar da gagarumin sauyi a fadin duniya. Hakan ne ya sa ake samun mutane masu zaman kansu ko kuma mujami'un coci da ke tafiyar da harkar ilimi a duk sanda gwamnati ta janye hannunta a aikin ba da ilimi. Lutz Möller, jami'in hukumar kula da ilimi da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO a Jamus shi kuma ya lura da haka inda ya ce:
"Domin hana kebe bukatun 'yan gata masu hannu da shuni da kuma kau da nuna wariya ga 'ya'yan talakawa akwai bukatar gwamnati ta samar da kyakkyawan tsari na ilmi ga al'uma."
Claudia Lohrenscheit ta ce a baya ga samun ilmi akwai bukatar samun kwarewar aiki wanda shi kuma hakki ne na rayuwa da ake bukatar tabbatar da shi. A cikin wani kamfen ba da ilimi da ya gudanar tun a shekarun 1970 Paulo Freire, jami'in ilmi na kasar Brazil ya gabatar da bukatar inganta shirin yaki da jahilci. To amma iya rubutu ko karatu ba zai iya samar da ingancin rayuwa ba face an alakanta shi da samun kwarewa. Lohrenscheit ta ce:
"Ya zamo wajibi ilmi ya jagorance mu ga tabbatar da ingancin rayuwar kanmu da kanmu. In ba haka ba bil Adama kansu za su yi watsi da hakkinsu na samun ilimi."
Tabbatar da wannan manufa ta ilimi alhaki ne da ya rataya a wuyan gamayyar kasa da kasa wadanda ya zamo wajibi su himmatu wajen ba da ingantaccen ilimi ga mutanen da ke fama da talauci ko kuma suke fuskantar wariya, ko kuma suke zaune a yankunan da ake rigingimu a cikinsu. Claudia Lohrenscheit ta kara da cewa ba da ilmi ga marasa galihu mizani ne da ake amfani da shi wajen kimanta wayewa da kuma ci gaban al'uma.
Samun damar zuwa makaranta hakki ne ga kowa
Katharina Tomaschevski, tsohuwar jami'ar Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da hakkin bil Adama na samun ilmi ta gabatar da wata bukata da ta nemi tabbatar da hakkin bil adama na samun ilmi da ke kunshe da manufofi guda hudu da suka hada da ba da ilmib da samun damar zuwa makaranta da amfani da ilmi da kuma amincewa da duk wani wani nau'i na ilimi daidai da dokokin kare hakkin bil Adama.
Lutz Möller ya ce a nazarin da ta yi a kasashe da dama hukumar UNESCO ta gano matsalar rashin zuwa makaranta a yankuna da dama na duniya da talauci ya yi wa katutu, inda ta yi misali da wasu yankunan karkara da ake samun makarantu masu ba haya guda wa dalibai maza da mata-dalilin da ya sa 'yan mata ke kin zuwan makaranta walau sabo da dalilai na kiyaye kansu ko kuma sabawar hakan da al'ada.
Bukatar samun ilmi mai inganci
A shekarar 2000 hukumar UNESCO ta gudanar da wani taro a birnin Dakar na kasar Senegal inda kasashe 164 suka daidaita kan bukatar cimma muhimman muradu guda shida da ba da ilmin firamare kyauta ga dukan yara a fadin duniya kafin shekarar 2015 ke zama daya daga cikinsu. To amma akwai yara miliyan 70 da suka isa shekarun zuwa makaranta da har yanzu ba su karatu. Wannan matsala ta ma fi kamari ne a yankin kudu maso gabashin Asiya da kudancin Asiya da yankin kudu da hamadar Sahara. To amma Lutz Möller ya gano daidetuwar yawan maza da mata da ke zuwa makarantar firamare tamkar wata gagarumar nasara.
Ita dai hukumar UNESCO rashin ingancin ilmi na daga cikin kalubaken da take fuskanta kasancewar kwararrun malamai da yawansu ya yi kasa da miliyan biyu ne a fadin duniya ke karantar da yaran da yawansu ya fi karfinsu. Akwai kuma bukatar samar da littatafai da sauran kayan aikin karatu wa makarantu. Hukumar UNESCO ta jadadda wannan bukata a shekarar 2011 inda ta yi kira ga kasashe masu hannu da shuni da su ba da gudunmuwar kudi domin magance wannan matsala. Hakazalika Lutz Möller ya ce akwai bukatar kowace kasa ta samar da karfaffen tsari madawwami ta kuma shawo kan matsalar karancin kayan aiki da za a fuskanta nan gaba.
Mawllafi: Ulrike Mast-Kirschning/Halima Abbas
Edita: Umaru Dan-Ladi Aliyu