Yara kanana da ke aikin soja da kuma sadaukar da rayuwarsu
Ba su fi shekaru bakwai zuwa takwas da haifuwa ba, ana tilasta su shan kwayoyin sa maye, suna daukar makamai don kisan jama'a. Yaran na lalata makomar rayuwarsu. Kadan daga cikinsu ke komawa rayuwarsu ta asali
Fadawa cikin tashin hankali
Dakunan dabam ya ragargaza, iyalan da aka hallaka danginsu ko kuma abokanensu suka jikkata. A yanzu yara na shiga yakin basasa misali abinda ke faruwa a birnin Aleppo na kasar Siriya da wuya bai tabi hankalinsu ba. Yara da yawa sun fada cikin tashin hankalin. Dole ne kuma su shiga yakin da ke barazana ga kasarsu domin su kare rayuwarsu.
Da sunan ta'addanci
'Yan ta'addan kungiyar IS basa shayin cin zarafin yara kanana. A cewar Majalisa Dinkin Duniya kungiyar na amfani da yaran a matsayin masu kai harin kunar bakin wake, ko kuma garkuwa da su lokacin yaki. Wasu ana tilasta musu kisan mutane. Duk da cin zarafin jama'a, amma matasa na sha'awar kungiyar IS.
Ba a fagen daga kawai ba
A cewar asusun kula da yara kanana wato UNICEF, ana tilasta wa samari da 'yan-mata shiga aikin soja, kana su dauki makamai su yi yaki, irin wadannan yaran walau dai marayu ne, ko sayar da su aka yi, ko kuma yaki ne ya raba su da iyayensu. Daga nan suke shiga kungiyar, a sa su fagen daga ko ma ana lalata da su.
Yara 250.000 ke tsundum cikin yaki
Kama daga Sudan, Somalia, Sudan ta Kudu da Chadi, wadannan wasu daga cikin kasashen da yara suka shiga yakin basasa cikin shekarun da suka gabata. Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa yara 250.000 sojoji ko 'yan tawaye suka tilasta musu shiga yaki. A rahoton Majalisar Dinkin Duniya, bangarorin yaki 52 cikin kasashe 23 ake cin zarafin yara.
Bisa shan maye suke biyyaya
Aiki da yara na da mahimmanci ga kungiyoyin mayaka. Ninja Charbonneau ta asusun UNICEF a hirar ta da DW, ta ce akwai riba wajen yaki domin yaran na da saukin a juya musu hankali. "Sau tari akan shayar da su ababen maye da yi musu zakin baki kana da nuna musu fina-finai don su yi imani da abinda ake umartansu". Suna kasancewa a tsorace ko wane lokaci, idan sun sabawa mayakan za a iya kashe su.
Taimakon dakarun kiyaye zaman lafiya
Wasu lokutan yaran na tserewa ko kuma dakarun gwamnati na kubutar da su. Wannan budurwar na mika makamanta ga dakarun kiyaye zaman lafiya na MDD. Daga karshe za a bata abinci da magani. Yaran da ke shiga soja na fiskantar akasari karancin abinci, raunukan a jikinsu, cututtukan da ake samu ta jima'i, matsalar kwakwalwa da kuma dogaro da shan kayan maye.
Komawar rayuwa yadda ya kamata
Yaran an bata su da kyar suke iya mantawa da abinda kwakwalwarsu ta koya a yaki. Don haka cikin dari-dari suke yinsa. Don haka yana da muhimmanci, a sake maida su cikin al'umma. A sansanonin yaran na zuwa makaranta, har lokacin da suka koma cikin iyalansu. Ko da shike wannan yana matukar bukatar lokaci, kana yana da wuya, ko da kuwa bayan an kawo karshen tashin hankalin.
Kokarin mantawa da abinda suka koya
Daya daga cikin wanda ta yi nasara ita ce China Keitetsi. A matsayinta na marubciya, ta na kokarin mantawa da mummunan rayuwar da ta gani, a matsayinta na tsohuwar mai yaki cikin kasar Yuganda, kamar yadda ta rubuta cikin littafin ta mai suna "Hawaye daga Sama har kasa". Ta yi shekara guda a Denmark bayan kubuta, inda ta yi kokarin mantawa da ta'asar da ta gani a rawuya mafi muni da ta koya.
Rayuwa cikin farin ciki
Shi ma Emmanuel Jal ya taba shiga aikin soja. A yanzu ya kasance fitaccen mawakin zamanin na Hip-Hop. A fitowarsa yakan bayyana rayuwa cikin jin dadi, ko da yake ba zai taba mantawa da mummunar rayuwa da ya taba kasancewa a ciki ba. Wakokinsa na tunatar da yakin basasan kasar Sudan. Inda yace " Bisa rubutatattun wakoki, mutum zai kawo hadin kai da yafewa juna" Haka dai dan fafitikan ya fada.
Jan Hannu
Wannan shine alamar kudurin MDD kan ceto yara da suka tsunduma a yaki, inda kasashe 150 suka sa hannu kan kudurin,kuma a ranar 12.02.2002 kudurin ya fara aiki. Tun wannan lokacin aka yi wa wannan ranar lakabin "Ranar Jan Hannu" domin tunawa da makomar yara a kasashe da dama.
Yaushe ne yaro yake yaro?
Ga kudurin yancin yara a sherara 1989 duk wanda ke fagen yaki dan kasa da shekaru 15, a matsayin yaro yake. A shekarar 2002 aka kara shekarun da mutum zai iya kare kansa a yaki to ya kai shekaru 18. Daukar mayaka don radin kansu, daga shekaru 14 a bisa doka yake da. Amma ga kungiyoyin kare yancin jama'a duk dan kasa da shekaru 18 a yaki, suna daukarsa a matsayin yaro da ke aikin soja.