Tattalin arziki
Dakile kudaden fito tsakanin kasashen Turai da Japan
July 17, 2018Talla
Kasar Japan da kungiyar Tarayyar Turai sun kulla sabuwar yarjejeniyar kasuwanci da za ta shafi kashi daya bisa uku na tattalin arzikin duniya.
Masharhanta na ganin wannan a matsayin martani ga manufofin Shugaba Donald Trump na Amirka wanda ya dauki matakan kare harkokin kasuwanci na Amirka. Karkashin sabuwar yarjejeniyar za a zabtare galibin kudaden fito tsakanin kasashen Turai da Japan da kimanin kashi 99 cikin 100 daga kayayyakin da suke fitowa daga Japan zuwa Turai, sannan kimanin kashi 94 cikin 100 daga kayayyakin kasashen Turai da ake kai wa zuwa kasar Japan.