Washington zata janje daga Afghanistan
February 29, 2020Talla
Shugaba Donald Trump na Amirka ya yi kira ga al'ummar Afghanistan da su bayar da damar samar da zaman lafiya a wannan kasa, bayan shekaru 18 na tashin hankula. Tun a jiya Jumma'a nedai Trump ya sanar da wakilcin sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo a wajen rattaba hannun na Qatar, a yayin da sakataren tsaro Mark Esper, zai gabatar da sanarwar hadin gwiwa da gwamnatin Kabul.
Ana saran yarjejeniyar kazalika, ta jagoranci daidaitawa tsakanin gwamnati da mayakan Taliban, wanda idan aka yi nasara, zai kawo karshen yakin da ya daidaita Aghanistan din na tsawon shekaru.