1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Wawason Ƙasashe: Yadda Jamus ta faɗaɗa daularta a Afirka

March 27, 2024

Jami'an mulkin mallakar Jamus a Namibiya irin su Adolf Lüderitz, sun samo filaye ta hanyar kwantaragi da shugabanni na gargajiya. Sai dai kwantaragin na hade da yaudara.

https://p.dw.com/p/4eCOJ
Lüderitz a kasar Namibiya
Hoto: picture-alliance/dpa/T. Schulze

A shekarar 1885, Adolf Lüderitz ya mallaki wurare da dama a inda yanzu ake kira da ƙasar Namibiya. Amma akwai rashin gaskiya a irin yarjejeniyar da ya yi da mazauna wurin, ta yadda har jami’an mulkin mallaka na Jamus sai da suka yi shakka a kanta.

Ta yaya Jamus ta fara kafuwa a inda yanzu ake kira Namibiya?

A shekarun 1880, Turawa masu fitar da taswira sun san cewa akwai wurare uku kacal da za a iya ya da zango a jiragen ruwa a gabar teku mai tsawon kimanin kilomita 2,000 (misalin mil 1,242). Yayin da matafiyan suka fito daga jiragen ruwan, sai suka kwashi kimanin kilomita 140 na sahara, yawancin inda ba kowa, da ta nausa ta yi ciki: saharar Namibiya ke nan.

Wani Shugaban al’umar Nama, Josef Fredericks na II, ya karɓi baƙuncin wani matashin ɗan kasuwa ɗan kasar Jamus mai suna Heinrich Vogelsang a Bethany, a kudancin Namibiya a shakarar 1883.

A madadin ɗan kasuwar Jamus Adolf Lüderitz, Vogelsang ya yi wa Fredericks tayin bindigogi 200 da Fam ɗin Ingila 100 da sunan wani ɗan kasuwar Jamus da ake kira Adolf Lüderitz, a kan mallakar wani yanki da ba kowa a gaɓar Tekun Atlantika. ‘Yan watanni bayan wannan sai wata yarjejeniyar ta biyo baya: ta bindigogi 60 da kuma Fam ɗin Ingila 500 a kan faɗin ƙasa da ya kai mil 20 daga gaɓar Tekun, wadda ta tafi har zuwa Kudancin Kogin Orange, da ya yi iyaka da ƙasar Afrika Ta Kudu.

Me ya sa wannan cinikin filin yake da ruɗani haka?

Awon da ake amfani da shi a wajen na mil ɗin Ingila ne, daida da kilomita 1.6 a wancan lokacin. A lokacin ba a san awon kilomita bisa Nazarin Kasa ba — kuma wannan ita ce yaudarar da aka yi a kwantiragin. Domin mil na nazarin ƙasa irin na Jamus da ɗan kasuwar yake nufi ya kai kilomita 7.4, a taƙaice ninki shida ke nan na abin da aka saba da shi!

Shi Lüderitz, da Vogelsang, da Turawan mishan da suka shaida cinikin sun san cewa Fredericks bai san faɗin filin mutanensa da ya sayar bisa rashin sani ba.

Ta yaya filayen da ɗaiɗaikun Jamusawa suka saya a Afirka ya zama mallakar Jamus?

Daga baya, ƙasar Jamus ta karɓe ikon ƙasa da ɗaiɗaikun Jamusawa suka mallaka a Kamaru da Kudu Maso Yammacin Afrika da kuma Gabashin Afrika.

A taswirar mulkin mallaka, Lüderitzland ta bayyana, sannan kuma a watan Agusta na shekarar 1884, Jamus ta ayyana Lüderitzland a matsayin keɓaɓɓen yankin mulkin mallaka. Wannan wani babban mataki ne na burin Jamus na ta samar da wata gundumar mulkin mallaka.

Lüderitz ya yi fatan tsintar dami a kala a sayen ƙasar da ya yi a hamadar Namibiya, ta hanyar haƙo ma’adanai kamar tagulla. Wani lokaci a baya, ya taɓa mallakar dukkanin gaɓar teku ta wurin da ake kira Namibia a yau. Amma bai sami wani abu mai daraja ba, don haka sai ya talauce.

Lüderitz ya sayar da abin da ya mallaka ga Ƙungiyar ‘Yan Mulkin Mallaka Ta Jamus a shekarar 1885, sannan ya ɓace a wani yawon buɗe idanu da ya fita kwanaki kaɗan bayan sayar da kayan.

A ina ne kuma aka yi amfani da yarjejeniya don a mallaki ƙasa?

Dukkan yarjejeniyoyin da aka sa wa hannu a nahiyar ko dai ba a fahimce su sosai ba, ko ba a ɗauke su da wani muhimmanci ba, ko kuma an amince da su ne bisa wani tsari na gangan. A Kamaru, ta kai ga Jami'an Jamus sun goge ko sun yi watsi da buƙatun shugabannin wuraren suka yi a Yarjejeniyar Jamus da Duwala ta shekarar of 1884.

A ƙarshen shekarun 1884, Carl Peters, ba tare da umarnin gwamnatin Jamus ba, ya yi ta yawo cikin ƙasar Tanzaniya ta yanzu, yana neman shugabannin da ke wurin da su sa hannu a kan wata takarda da ya rubuta da Jamusanci. Da yawan lokuta ma sai ya bugar da su da barasa, an yi wa sarakunan alƙawarin samun kariya daga Jamus.

Me ya sa ƙasar Jamus daga baya ta amince da waɗannan yarjeniyoyi?

Abu ne mai wuya a ce mutum kamar Shugaba von Otto von Bismarck, wanda a farko ma yake da shakku a kan samun Gundumomin mulkin mallaka da Jamusawa suke yi, kuma ya zo yana amincewa da tsare-tsaren wasu ‘yan kasuwa masu ra'ayin kama-karya, kamar su Carl Peters, da Adolf Lüderitz, ko Adolph Woermann.

Amma a tsakiyar shekarun1880, ƙasahen Turai sun yi wawason ƙasashe a Afrika. Misali, Peters, ya dage a kan cewa muradun kasar Belgium a Afrika Ta Tsakiya za su iya karya shirin Jamus. Bismarck dai sai ya bayar da kai bori ya hau bisa dalilai na siyasa don bayar da dama ga buƙatar Peters na kare iyakokin ƙasashen da suka mallaka.

Mene ne ainihin manufar ‘mallakar ƙasa'?

Irin waɗannan yarjejeniyoyi kariya na ƙarya, an yi su ne da sunan za a ba wa mazauna wajen da suka sa hannu a yarjejeniyar kariya daga Jamus, muddin suna yi wa ƙasar Jamus ɗin biyayya. Amma a zahiri an yi amfani da su ne kawai don birnin Berlin ya tabbatar wa da sauran ƙasashen Turai, abokan hamayyarsa, iƙirarinsa na mallaka gundumomin mulkin mallaka, a hukumance, kuma hakan na nufin cewa Jamus za ta kare waɗannan wurare da ta mallaka. Muhimmin abun shi ne sauran ƙasashen Turai su amince da irin waɗannan yarjejeniyoyin, amma idan aka zo maganar mutunta yarjejeniyar dangane da mutanen Afrika, Jamusawan da suka sa hannu a yarjejeniyar yawanci ba sa adalci ko kuma suna nuna son rai.

Yarjejeniyoyin ba da karika sun ba wa kamfanonin Jamus damar mallakar filaye, da ma'adanai, da kuma biyan ma'aikata abin da bai taka kara ya karya ba, da kuma samun damar jibge sojoji da makaman Jamus.

Me ya sa shugabanin Afirka suka sa hannu a takardun yarjeniyoyin?

Akwai shakku a kan cewa shugabanni a ƙasashen Tanzaniya, da Namibiya, da Togo ko Kamaru sun fahimci abin da suka sa hannu a kai. Wasu shugabannin sun buƙaci makamai ne don su yi ramuwar gayya a kan abokan faɗansu. Wasu kuma, kamar shugabanin Duwala ta ƙasar Kamaru, sun ga an cire bukatunsu daga cikin samfurin yarjejeniyar Jamus, a wasu mas’alolin kuma, ‘yan mulkin mallakar Jamus, suna ganin cewa suna da goyon bayan manyan makamai da ƙwararrun sojoji, sai kawai suka yi biris da yarjejeniyoyin da aka ƙulla.

Mene ne sakamakon hakan ga mazauna/mutanen Afirka?

An bar wa wasu tsirarun ‘yan mulkin mallakar Jamus damar gudanar da mulkin gundumomin da aka mallaka. Ba wani daga cikinsu da yake da tunanin taimaka wa mazauna wuraren ko ci gabansu, kuma yawancinsu sun yi amfani da ƙarfin soja wajen murƙushe duk wani yunƙuri na ƙin yarda da su, sannan sun yi amfani da ƙarfin soja wajen sa wa a yi musu ayyuka kamar na gine-gine da noma.

DW, Gidan rediyon Jamus da yake yaɗa shirye-shirye a duniya ne ya shirya shirin Illolin Mulkin Mallakar Jamus, wanda Ofishin Kula Da Harkokin Ƙasashen Waje Na Jamus (AA) ya ɗauki nauyi. Ƙwararru a ɓangaren tarihi da aka tuntuɓa su ne Farfesa.

Lily Mafela da Farfesa Kwame Osei Kwarteng da Reginald Kirey.