An hau idi a Makka da Najeriya
July 6, 2016Talla
Miliyoyin Musulmai a kasa mai tsarki ta Saudiyya da ma wasu kasashe kamar15 na Musulmi da ke zama Larabawa da wasu sassan duniya sun gudanar da sallar idi ta karamar salla a ranar Laraban nan.
A kasar Indonesiya da ke da yawan al'umma miliyan 250 da kuma ke zama kasar da tafi yawan mabiya addinin na Islama a duniya, miliyoyin wadannan al'umma ne suka fita sallar ta idi babban masallancin Al Azhar a Kudancin birnin Jakarta a ranar Laraba, da ke zama cikin kwanaki biyar da kasar ta ware na hutu duk da irin fargaba ta masu ikirarin Jihadi da ke kai hare-hare.
An dai tsara irin wannan ibada a wannan rana a wasu kasashen irinsu Bahrain da Masar da Jordan da Iraki da Najeriya da sauransu.