Yawaitar kashe-kashe a Sudan ta Kudu
September 6, 2022Wani rahoto da MDD ta fitar a wannan talata ya nunar da cewa kimanin fararen hula 173 ne aka kashe tare da yin garkuwa da 37 cikin watanni hudu a Sudan ta Kudu a fada da ke gudana tsakanin dakarun da ke biyayya ga shugaba Salva Kiir da mataimakin shugaban kasar Riek Machar.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikicin ya shafi akalla kauyuka 28, kuma ya sa mutane kusan 44,000 tserewa daga kauyukansu. Sannan ta kara da cewa bangarorin Salva Kiir da Riek Machar ne ke da alhakin take hakin bil-Adama da ke wakana a kasar.
Tun bayan samun ‘yancin kai a shekara ta 2011 ne Sudan ta Kudu ke fama da rikice-rikice na siyasa da kabilanci, wanda ya hana ta murmurewa daga yakin basasar da ya yi sanadin mutuwar kusan mutane 400,000 tare da raba miliyoyi da muhallinsu a tsakanin 2013 da 2018.