1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Yawan 'yan takara a 2023

Uwais Abubakar Idris LMJ
May 5, 2022

'Yan takara da dama ne ke ci gaba da yin tururuwa a Najeriya, wajen fitowa takarar neman shugabancin kasar a zaben da za a yi a badi.

https://p.dw.com/p/4AsR9
Afiika I Najeriya I APC I Abuja
Jam'iyyar APC ta fi kowa yawan 'yan takara a Najeriya, duk da tsadar takardar tsayawaHoto: Ubale Musa/DW

A wannan karon dai an samu tarin masu aniyar yin takarar shugabancin kasar fiye da kowanne lokaci, abin da ya bai wa jam'iyyun siyasa musamman APC mai mulki da babbar jam'iyyar adawa ta PDP dama ta samun makudan kudi daga takardun neman shiga takara. Bayanai na nuni da cewa jam'iyyar APC mai mulki ka iya samun Naira biliyan 30, kasancewar kowane dan takara na biyan Naira miliyan 100.

Amfani da kudi masu yawan gaske na tattare da al'ada ta siyasar Najeriyar, domin duk da koma bayan tattalin arziki da kasar ke fuskanta da zarar an kada kugen siyasa zabe ya karato zaka ga 'yan siyasa sun zaburo ana lalle Naira. To sai dai a cewar Mallam Abubakar Ali masani a fannin tattalin arziki, ya kamata a yi hattara ga yadda ake ruwan kudi na sayen takaradun neman takara a zaben na Najeriya da a zahiri suka wuce kima.