Amirka ce a kan gaba wajen yanwan masu Coronavirus
March 28, 2020Yawan wadanda suka kamu da cutar Coronavirus yanzu ya kai sama da mutane dubu 600 a fadin duniya. Hakan ya faru ne bisa yadda cutar ke kara bazuwa a Turai da Amirka, inda a wannan Asabar din aka samu karin sabbin alkaluman mutanen da suka kamu da cutar a kasashen duniya da yawa.
Wasu akaluma da jami'ar John Hopkins ta fitar, sun nuna cewa akwai sauran jan aiki na yakar wannan cutar. Akaluman jami'ar dai sun nuna cewa mutane akalla dubu 27 ne suka mutu sakamakon annobar Coronavirus. A yanzu haka dai kasar Amirka ce ke da mafi yawan mutanen da suka kamu da ita, inda aka tabbatar Amirkawa kimanin dubu 104 ne suka kamu da cutar, yayin da kasashe biyar da ke bin bayan Amirka a yawan mutanen da suka mutu suka hada da Italiya da Spain daChina sai kuma Faransa.