Yawan mutanen da suka mutu a ambaliyar ruwan Koriya Ta Arewa ya ninka
August 26, 2007Talla
Gwamnatin Koriya Ta Arewa ta ce yawan mutanen da suka rasa rayukan su sakamakon ambaliyar ruwan da ta auku a kasar a makon da yagbata ya ninka adadin da aka bayar da farko har sau biyu. Kamfanin dillancin labarun kasar ta Kwaminis KCNA ya ce akalla mutane 600 suka mutu ko suka bace a wannan ambaliya. Kamfanin na KCNA ya rawaito ma´aikatar kididdiga a birnin Pyongyang na cewa wasu dubban mutane sun samu raunuka. Kawo yanzu dai gwamnati kasar ta ce mutane 300 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu dubu 300 suka yi asarar gidajensu, kana kuma sama da kashi 15 cikin 100 na gonakin shinkafa da masara sun lalace.