Yaya fafatawar kungiyoyi 18 na Bundesliga za ta kasance a 2017-2018?
Wace kungiyar za ta lashe Bundesliga, wadanne kungiyoyin za su shiga gasar cin kofin zakarun Turai, ko na UEFA, su wa za su sauka rukuni na biyu? Wannan shi ne hasashen da muka yi kan yadda za ta kaya a 2017-2018.
Kungiyar Bayern Munich
Bundesliga wata gasa ce wadda kungiyoyi 18 ke fafatawa a wasanni 34 da kusan kullum Bayern ke lashe ta daga karshe. Hakan ta faru akalla sau 27. A bana kungiyar ta sayo Corentin Tolisso a miliyan 40 na Euro da ke zama dan wasa mafi tsada a tarihinta, kuma burinta na lashe gasar har kullum bai canza ba. A hasashen DW ma dai ko a wannan karo kusan ba tababa Bayern ce za ta lashe Bundesligar.
Kungiyar RB Leipzig
Baki a Bundesliga, amma a bara sun yi wa Bayern dan galadima tare da samun cancantar shiga gasar cin kofin zakarun Turai. Sai dai a bana ko za su iya ci gaba da mutunta akidarsu ta amfani da matasan 'yan wasa, da jure wa wahalar wasannin Turai? Hasashen DW: Za su iya shiga jerin kungiyoyi biyar na fako a Bundesliga, amma zai wuya su cancanci buga kofin zakarun Turai kai tsaye a wannan karo kuma.
Julien Nagelsmann mai horas da 'yan wasan Hoffenheim
Mai horas da 'yan wasa mafi karancin shekaru a Bundesliga, ya yi nasarar shigar da Kungiyar Hoffenheim a gasar cin kofin zakarun Turai a karon farko a tarihi. Nagelsmann wanda aka zaba a matsayin mai horas da 'yan wasa mafi kwarewa a bara, mutum ne mai fasahar iya shirya kungiyarsa zuwa daga. A kan yi wa kungiyarsa buri daya da Leipzig. A hasashen DW, Hoffenheim za ta zo cikin biyar na farko.
Kungiyar Borussia Dortmund
Kakar wasan bara ta zo wa kungiyar da rudani: Ga tarzomar magoya baya, ga hari kan motar 'yan wasa, ga canjin mai horas da 'yan wasa. Sabon nadi Peter Borz na da nauyin kawo sauyi da ma na lashe Bundesliga. Da ya jagoranci Ajax ya bayar da fifiko ga wasan kai farmaki da salon wasan Johan Cruyff. Hasashen DW: Idan Aubameyang da Mario Götze ba su bar Dortmund ba, za ta iya zuwa a uku na farko.
Kungiyar FC Kolon
A karon farko bayan shekaru 25 Kolon ta yi nasarar sake shiga wasannin Turai. Sai dai tafiyar Anthony Modest daga kungiyar ta rage azamar da take da a bara. Ba a san yadda za ta fuskanci wasannin na bana ba, ba tare dan wasanta da ya ci mata kwallaye 25 ba a gida da ketare a bara ba. Amma dai sun tsira da mai horas da 'yan wasansu Peter Stöger. A hasashen DW a bana burinsu zai kasance takaitacce.
Kungiyar Hertha Berlin
Cali-calin Hertha Herthinho na da alama cike da farin cikin shigar kungiyarsa wasannin Turai. A kakar bara kungiyarsa ba ta yi nasarar shiga wasannin Europa League ba. Amma a bana za ta buga akalla wasanni uku a waje. To wace sa'ar Hertha ke da a Bundesliga? A hasashen DW akwai kungiyoyi da dama da suka fi karfinta, don haka sake samun nasarar cancanta shiga wasannin Turai zai yi wuya sosai.
Kungiyar Freiburg
Mafarkinsu na shiga wasannin Turai a bana bai tabbata ba. Freiburg ta sha kashi a Siloveniya a hannun Kungiyar Domzale a wasan tankade na neman shiga wasannin Turai. Amma yanzu mai horas da 'yan wasan kungiyar Christian Steick da kungiyar tasa na iya maida hankali wajen sake hawa matsayin shiga wasannin Turai na badi. A hasashen DW hakan zai yi wuya domin kungiyar na da rauni sosai.
Kungiyar Werder Bremen
A kakar cinikin 'yan wasa da ake ciki, Werder ta saye a karon farko dan wasa daga Chaina: Yuning Zhang. Sai dai ba zai iya maye gurbin 'yan wasan da suka bar kungiyar ba. Mai tsaron gida Felix Wiedwald, da Kaptain Clemens Fritz da Claudio Pizzaro sun fice zuwa wasu kungiyoyin. A hasashen DW Bremen za ta fuskanci koma-baya, amma za ta samu akalla karin magoya baya a kasashen gabashin duniya.
Kungiyar Borussia Mönchengladbach
Ko kungiyar na bukatar sanya albarkar Paparoma? Bayan da ta kare a matsayin ta tara a kakar bara, ba bu alamar za ta iya wuce wannan matsayi ko a bana. A fannin kudi ba za ta iya ja ba da su Bayern, Dortmund ko Leipzig. Amma ko za ta iya ja da su a filin wasa? A hasashen DW ba za ta iya shiga gasar cin kofin zakarun Turai ba, amma za ta iya kwatanta shiga Europa League.
Kungiyar Eintracht Frankfurt
A wasannin farko na kakar bara Eintracht Frankfurt ta fara shiga gasar da kafar dama. Sai dai zuwa tsakiyar kakar ta kasance kamar kazar da kwai ya fashe mata a ciki. A kakar bana burin kungiyar shi ne samun cancantar shiga wasannin Turai. A hasashen DW kuwa, ko a bana akwai alamar tarihi ya maimaita kansa.
Kungiyar Schalke
A lokuta da dama burin da ake saka wa kan kungiyar Schalke na zamowa mafarki kawai. A kakar bara ta kare a matsayin ta 10. Rabon da ta hau wannan mummunan matsayi tun a shekarun 1990. Ta yi canjin masu horas da 'yan wasa har sau biyar a cikin shekaru uku. Ko Domenico Tedesco na yanzu zai iya farfado da martabar kungiyar? A hasashen DW, in sun yi kokari za su iya shiga gasar Europa League.
Kungiyar Bayer Leverkusen
Bayer Leverkusen ta dauki matakin canza salon tafiya a bana. Roger Schmidt ya koma Beijing, Seven Bender ya bi sahun wansa Lars. Ba zato ne kungiyar ta nada Heiko Herrlich a matsayin mai horas da 'yan wasanta. Da kyar da jibin goshi ta tsira daga sauka daga Bundesliga a bara, a bana burinta kaiwa ga cancantar shiga wasannin Turai. A hasashen DW za ta iya karewa a tsakiyar teburin Bundesliga.
Kungiyar FC Augsburg
Wannan hoto kadai na cike da bayani na matsalar da kungiyar Augsburg take ciki. Ko kungiyar za ta zamo kurar baya a watan Mayu? Tare da sabbin zuwa Bundesliga wato Stuttgart da Hannover. Zai dai wuya Augsburg ta kai labari a wannan shekara. Sai kungiyar Manuel Baum ta sadaukar da kanta baki daya a ko wani wasa. A hasashen DW Augsburg za ta tsinci kanta a cikin kokowar 'yan baya na Bundesliga.
Kungiyar Hamburger SV
Hamburg ita ce kungiya daya tilo da ba ta taba sauka daga Bundesliga ba tun daga lokacin kafa gasar a shekarar 1963. Amma ta ji jiki a shekaru hudu na bayan nan inda sau biyu take kusa ga sauka amma ta tsira da kanta a wasan kalubale na karshe. Ko yaya za ta kasance mata a bana? Mai horas da 'yan wasa Markus Gisdol mutum ne mai nutsuwa da basira. A hasashen DW Hamburg za ta sha ko a wannan karo.
Kungiyar FSV Mainz 05
Bayan da Mainz da ta yi nasarar ketara siradin sauka daga Bundesliga a bara, a bana za ta sake lale. Bayan samun sabon shugaba da sabbin tufafin jersy na wasa, kungiyar ta dauki sabon mai horas da 'yan wasa da sabon mai tsaron gida wato Sandro Schwarz da Rene Adler. A hasashen DW ko a bana ma za ta fuskanci barazanar sauka daga Bundesliga matsawar ba ta gyara kura-kuranta ba.
Kungiyar VfB Stuttgart
Sun lashe gasar Bundesliga sau uku a baya. Amma a bara sun shekare a Bundesliga ta 2. A bana sun sake hawa Bundesligar. Stuttgart ta karfafa matasan 'yan wasanta da wasu kwararru biyu da ke buga wa kasar Jamus wasa, mai tsaron gida Ron-Robert Zieler da mai tsaron baya Holger Badstuber daga Bayern Munich. A hasashen DW ba barazanar sauka, tana ma iya zuwa a tsakiyar teburin na Bundesliga
Kungiyar Hannover 96
Tashen da Hannover ta yi tun bayan kafuwarta bai tsaya ga batun wasanni ba kadai. Za ta rasa rinjaye na hannun jarinta idan Martin Kind ya karkare cinikinta. Hakan kuma zai kawo karshen tsarin nan na Jamus wanda ke bai wa kungiya damar mallakar rinjaye na hannun jarinta zai kau. Wannan ya sa magoya bayan kungiyar ke hushi da ita. A hasashen DW rigingimunta za su sa ta sauka daga Bundesliga.